Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ba Sanata Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu) kwana 21 ya kawo mata tsohon Shugaban Hukumar Fansho, Abdulrasheed Maina.
Ndume, wanda shi ne Sanata mai wakiltar mazabar da Maina ya fito, ya karbi belin Maina ne bayan kotu ta shardanta cewar sai Sanata mai ci ya tsaya masa kafin ta ba da shi beli, sannan sanatan ya kuma kawo shi kotu a duk lokacin bukatar hakan ta taso.
- Abin da ya sa na karbi belin Abdulrashid Maina —Ndume
- Matsalar tsaro: PDP ta kalubalanci Buhari kan kalaman Ndume
Sai dai tun da Ndume ya karbe shi, Maina bai sake zuwa kotun ba ballanta a ci gaba da shari’ar zargin da ake masa na wawure kudaden gwamnati.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ce ta kai Maina da kamfanin Common Input Properties & Investment Limited kara kan wasu zarge-zarge 12.
EFCC na zargin Maina da amfani da asusun kamfanin wajen karkatar da Naira biliyan 2 wadanda ya yi amfani da su wurin mallakar wasu kadarori a Abuja.
EFCC ta bude tuhumar da take yi wa Maina tare da gabatar da shaidu, daga ciki har da ’yan uwan Maina, amma tun ranar 29 ga watan Satumba bai sake halartar zaman kotun ba, lamarin da ya sa masu shigar da kara ke zargin cewar ya gudu ne.
Da aka zo sauraron karar a ranar 2 ga watan Oktoba, Ndume ya bayyana wa kotu cewar bai san inda Maina yake ba, kuma duk kokarin da ya yi na nemo shi ya faskara.
Daga nan Mai Shari’a Okon Abang, ya umarci Sanata Ndume da ya kawo wanda ake zargin cikinsu kwana 21.
Ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba, 2020.