✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da umurnin a saki Uzor Kalu

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta ba da umurnin sakin tsohon Gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu daga kurkuku. A watan Disamban…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta ba da umurnin sakin tsohon Gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu daga kurkuku.

A watan Disamban bara ne kotu ta yanke wa Uzor Kalu hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari bayan samun sa da laifi a badakalar Naira biliyan 7.1 na jihar Abia a lokacin mulkinsa.

A farkon watan jiya kuma Kotun Koli ta Najeriya ta soke hukuncin tana cewa alkalin da ya yanke shi ba shi da hurumin yin haka saboda an yi masa karin girma zuwa Kotun Daukaka Kara a lokacin.

Ta kuma ce amfani da sashe na 396(7) na Dokar Hukunta Manyan Laifuffuka ta 2015 da aka dogara da shi aka bai wa Mai Shari’a Mohammed Idris damar zuwa ya kammala shari’ar ya saba wa Kundin Tsarin mulkin Najeriya.

An gurfanar da Uzor Kalu ne tare da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da  kuma tsohon Daraktan Kudi na Gidan Gwamnatin Jihar Abia Jones Udeogu.

Daga bisani Udeogu ya daukaka kara zuwa Kotun Koli wadda ta soke hukuncin a watan Mayun 2020 bisa hujjar cewa kotun da ta saurari shari’ar da farko ba ta da hurumin yin hakan.

Kotun Kolin ta ce alkalin da ya saurari shari’ar ta tsawon shekaru 12 a Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a Mohammed Idris bar kotun bayan samun karin girma zuwa Kotun Daukaka Kara.

Saboda haka bai cancanci ya zama mai yanke hukunci a Babbar Kotun Tarayyar ba tunda yanzu shi ba alkalin kotun ba ne.

A ranar Talata lauyan Uzor Kalu, Cif Lateef Fagbemi ya bukaci Mai Shari’a Mohammed Liman ya ba da umurnin sakin tsohon gwamnan daga kurkuku bisa hukuncin da Kotun Kolin ta yanke kan daukaka karar da Udeogu ya yi.

“Muna mika bukatarmu bisa tanadin shashe na 159 na Kundin Dokar Shari’ar Manyan Laifuka.

“Mun yi hakan ne sakamakon hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar 8 ga watan Mayu,” inji Fagbemi.

A martaninsa, lauyan hukumar EFCC Rotimi Jacobs ya ce hukumar, mai yaki da cin hanci da rashawa ba za ta kalubalanci bukatar Fagbemi na neman a saki Kalu daga gidan yari ba.