Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin tsare tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Roshas Okorocha, kan zargin almundahanar.
Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin bayan hukumar EFCC mai yaki da Karya Tattalin Arziki, ta gurfanar da tsohon gwamnan kan zargin karkatar da Naira biliyan 2.9.
EFCC ta gurfanar da shi ne a kan zargin laifuka 17 tare da Anyim Nyerere Chinenye da wasu kamfanoni biyar.
Kamfanonin da ake zargin su tare su ne; Naphtali International Limited da Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited da Pramif International Limited da kuma Legend World Concepts Limited as a gaban kotun.
A ranar Talata ne dai jami’an EFCC suka je gidan Okorocha, wanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, inda suka tisa keyarsa zuwa ofishinsa bayan an kai ruwa rana na tsawon yini guda.
EFCC na zargin sanata dan kin zuwa ya halarci zaman kotu kan zargin da ake mishi.