Wata babbar kotu a kasar Iraqi ta ba da umarnin kamo Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump a kan kisan babban hafsan sojin kasar Iran da kuma Shugaban Rundunar ‘Yan Shi’a ta kasar Iraqi, a shekara 2020.
Alkalin babbar kotun ya ba da takardar izinin kamo Donal Trump ne a ranar Alhamis 7 ga watan Janairun 2021 a karkashin dokokin kasar ta Iraqi.
Sanarwar ta ce za a ci gaba da bincike domin gano ragowar masu hannu a harin da yayi sanadiyar mutuwar mutanen, ‘yan kasar Iraq ne ko kuma mutanen kasar waje ne.
A ranar 3 ga watan Janairun 2020 ne wasu tagwayen rokoki da Amurka ta harba a daura da filin jiragen sama na Baghdad a kasar Iraqi suka hallaka Qassim Suleiman, kwamandan rundunar sojin kasar Iran ta Quds da kuma Abu Mahdi Al-Muhandes, mataimakin shugaban rundunar Hashd al-Shaabi ta kasar Iraqi.
Umarnin da kotun na kame Trump na zuwa ne a daidai lokacin da yake cikin tsaka me wuya biyo bayan hargitsin da magoya bayansa suka tayar domin dakile kayen da ya sha a zaben kasarsa.