Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ba da umarnin a kai malama Zeenat, uwargidan jagoran mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, asibiti domin jinyar ta saboda cutar COVID-19 da ta kamu da ita.
Kotun ta umarci Hukumar Kula da Gidajen Yari a Jihar Kaduna ne bayan lauyanta da maigidanta wanda ake tsare da su tare a kurkuku, Femi Falana ya gabatar da sakamakon gwajin da ya nuna ta harbu da cutar.
A zamanta na ranar Litinin kotun ta ce a je a yi jinyar Malama Zeenat a daya daga cikin asibitocin Gwamnatin Jihar Kaduna da ke cikin garin Kadauna, kuma wanda ke wajen gidan yarin da ake tsare da ita.
A makon jiya ne aka samu labarin kamuwar Malama Zeenat wadda ke tsare a gidan yari a Kaduna, da COVID-19, sai dai zuwa ranar Juma’a, Kwanturola Gidajen Yari na Kaduna, Ibrahim Maradun ya ce ba su da labarin kamuwar ta da cutar a hukumance.
Sai dai ya tabbbatar cewa Hukumar Takaita Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta dauki jininta ranar Laraba amma ba a samu sakamakon ba a lokacin.
A zaman ci gaba da Shari’ar Zeenat da Sheikh El-Zakzaky, Mai Shari’a Gideon Kurada ya umarci gwamnatin Jihar Kaduna da su fara jinyar Malama Zeenat nan take daga cutar ta COVID-19.
Bayan zaman kotun, lauyoyin gwamnati jihar da masu kare El-Zakzaky da matar tasa sun tabbatar cewa matar jagoran Shi’an ta kamu da cutar.
Falana ya ce sun gabatar wa kotun sakamakon gwajin da ya nuna ta kamu da cutar tun kwana bakwai da suka gabata kuma tana bukatar a yi jinyar ta.
Ya ce ana jinyar matar malamin ne a cibiyar lafiya da ke gidan yarin, amma cibiyar ba ta da kayan jinyar masu cutar kuma likita ya tabbatar da hakan a gaban kotun.