Wata kotun majistare ta bayar da belin wasu ’yan uwan juna a kan N20,000 kowannensu bayan gurfanar da su a kan satar kaji uku.
Kotun ta dauki matakin ne bayan an garfanar da matasan su biyu kan zargin da satar kaji uku da kudinsu ya kai Naira 45,000 a yankin Okebola a Jihar Ekiti.
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Ba a Ɗaukar Hoton Alƙali a Kotu
- Hisbah ta kori jami’inta kan hada kai da masu ayyukan badala
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Celeb Leramo, ya shaida wa kotun da ke zamanta a Ado-Ekiti cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba da misalin karfe 2 na rana wadanda ake tuhumar suka sace kajin uku mallakin Akogun Yemisi.
Lauyan wadanda ake kara, Barista Gnenga Ariyibi, ya bukaci kotun da ta bayar da belin su.
Alkalin kotun, Saka Afunso, ya bayar da belin kowannen su akan kudi N20,000 da gabatar da mutum daya da zai tsaya masa, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba.