✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin wanda ya yi wa ’yar amininsa

A ranar Alhamis da ta gabata ce wata Kotun Majistare da ke Fika a Jihar Yobe a karkashin Mai shari’a Muhammad Y. Alangarno, ta ba da…

A ranar Alhamis da ta gabata ce wata Kotun Majistare da ke Fika a Jihar Yobe a karkashin Mai shari’a Muhammad Y. Alangarno, ta ba da belin Alhaji Dauda Mubi da ke Unguwar Mubia bisa tuhumar yi wa ’yar amininsa ’yar shekara 13 ciki.

A farkon watan Nuwamba ne dai Kungiyar Mata ta Kasa (NCWS) ta shigar da Dauda Mubi kara a kotun bisa zargin cin amana da yi wa ’yar amininsa ciki don kwato mata hakkinta.

A baya dai lokacin da aka shigar da karar kotu ta tura Alhaji Dauda Mubi  kurkuku don zaman jiran shari’a kan laifin da ake zarginsa.

Wata majiya ta ce ya samu karaya ne a kafa a kokarinsa  na gudu, bayan tura shi gidan yari, amma yanzu ganin kafar za ta iya lalacewa, kotun ta ba da belinsa don ya je ya kula da kafarsa.

A zaman kotun na ranar Alhamis, Mai shari’a Muhammad Y. Alangarno, ya ba da belin Alhaji Dauda Mubi don kula da kafarsa har zuwa ranar 3 ga watan Janairun badi don ci gaba da sauraron karar.

Yarinyar wadda aka sakaye sunanta cikin da wanda ake zargin ya yi mata ya kai wata takwas, lokacin da aka kai karar, kuma yanzu ta haihu har an yi suna.