Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Sansanin Alhazai na Kano ta ba da belin mutumin da ake zargi da yin garkuwa da diyarsa mai shekara hudu tare da neman kudin fansa daga matarsa.
Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin a lokacin da aka karanto tuhumar da ake yi masa.
- Ya yi garkuwa da ’yar cikinsa yana neman kudin fansa daga matarsa
- Dalibi ya gurfana gaban kotu bisa zargin garkuwa da budurwarsa
- An kama malami ya yi garkuwa da dalibinsa
Alkalin kotun, Sakina Aminu ta nemi wanda ake tuhumar ya kawo mutum biyu su tsaya masa daga cikin mutanen gari da kuma limami.
Daga nan ta dage zaman zuwa ranar 9 ga Disamba, 2020 don ci gaba da sauraron shari’ar.
A kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa mahaifiyar yarinyar ta kai kara ga ’yan sanda cewa an sace diyarta a ranar 29 ga watan Satumba kuma aka kira ta a waya ana neman ta biya Naira miliyan biyu kudin fansa ko a kashe ta yarinyar.
Bayan bincike ’yan sanda sun gano cewa mijinta kuma mahaifin yarinyar ne ke kiran ta kuma daga baya aka samu yarinyar da aka sace a tare da shi.