Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta soke zaben Sanatan Filato ta Kudu a Jihar Filato, Napoleon Bali, sannan ta ayyana Ministan Kwadago, Simon Lalong a matsayin sabon sanata.
Kotun dai ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, bayan ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ta soke nasarar Bali na jam’iyyar PDP.
- Gwamnatin Kano za ta kashe biliyan 40 wajen gina gadojin sama da wasu ayyuka
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga, sun kama wasu 19 a Filato da Kaduna
Lalong dai ya tsaya takarar ce a karkashin jam’iyyar APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, amma bayan an ayyana cewa ya sha kaye a zaben, Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya nada shi Minista.
A cewar kotun, jam’iyyar ta PDP ta saba umarnin kotu kan kin shirya manyan taruka a matakan Mazabu, Kananan Hukumomi da Jiha tun a shekara ta 2021.
A sakamakon haka ne kotun ta ce bai halasta PDP ta tsayar da ’yan takara ba a zabukan Jihar.
Kotun dai wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a E.O Williams-Daeoud, ta ce kotun baya ta yi daidai da ta ayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben saboda dukkan tarukan da PDP ta yi a Jihar ba halastattu ba ne.