✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta aike da matashin da ya zagi mahaifinsa gidan kaso

Kotun ta daure shi shekara daya, ko biyan tarar N10,000

Wata kotun majistare da ke Jos, babban birnin Jihar Filato ta aike da wani lebura mai shakar 35, Fwangmun Danung, gidan gyaran hali saboda samunsa da laifin zagi da cin zarafin mahaifinsa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa alkalin kotun, Mai Shari’a Tapmwa Gotep, ne ya yanke hukuncin ranar Alhamis, bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifukan da aka zarge shi da aikatawa.

Alkalin dai ya ba mai laifin zabin biyan tarar N10,000 ko kuma daurin wata shida ga laifin farko, sai wani wata shidan a laifi na biyu.

Mai Shari’ar ya ce hukuncin zai zama izina ne ga wadanda suke tunanin aikata hakan a nan gaba.

Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Frank Alex, ya shaida wa kotun cewa mahaifin matashin, Othniel Danu, ne kai karar dan nasa tun ranar 26 ga watan Disambar bara, ga ofishin ’yan sanda na Rantya.

Bayanai sun nuna wanda aka yanke wa hukuncin ya fitar da mahaifin nasa daga cikin gidansa ta karfin tsiya, sannan ya kira shi da mara amfani wanda ba ya iya tsinana komai.

Dan sandan ya kuma ce wanda aka yanke wa hukuncin ya kunna makamashin iskar gas tare da yin barazanar kone gidan gaba daya.

Ya kuma ce matashin ya bukaci mahaifin nasa ya ba shi Naira dubu 200.

A cewar Insfekta Frank, laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 377 da 379 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Filato.