✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ɗaure mutumin da ya damfari surukarsa zai ƙulla aurenta da Buhari

Ta ce a matsayinta na Amarya, ta yi ta dakon sabon angon nata Buhari ya zo ya ɗauketa amma ta ji shiru.

Wata kotun majistare a Minna da ke Jihar Neja ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗauri na shekara guda bisa zargin damfarar surukarsa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Malam Gambo Adamu ya riƙa shaida wa surukarsa cewar yana shirya aure tsakaninta da tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Surukar tasa, Sa’adatu Aliyu wadda bazawara ce ta garzaya kotu ne tare da koken cewa surukin nata ya yi mata wala-wala bayan karɓar kuɗin da suka kai naira miliyan biyar daga hannunta da sunan zai haɗa aure tsakaninta da tsohon Shugaban ƙasar.

Ta kara da cewa, mai laifin ya kuma bukaci ta kafa wata kungiya mai zaman kanta wadda za ta zama shugaba yayin da shi kuma surukin zai yi aiki a matsayin kakakin kungiyar, inda ya yi mata alkawarin cewa za ta samu tallafi daga Gwamnatin Tarayya da ta jihohi, baya ga kujerun aikin Hajji.

Ta shaida wa kotu cewa wata rana Gambo ya kai mata naira 100,000 a matsayin sadakinta, da huhun goro ɗaya da kuma soyayyiyar kaza da nufin cewa kyauta ce daga tsohon shugaban ƙasar, bayan ya yi mata ƙaryar ɗaura auren.

Ta ce a matsayinta na Amarya, ta yi ta dakon sabon angon nata ya zo ya ɗauketa.

Yayin da ba ta ganshi ba ne ta yanke shawarar kai surukin nata gaban kotun domin ta shiga tsakaninsu.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Musa Zago, ya ɗaure surukin nata wata 12 a gidan yarin, da zaɓin tarar naira 100,000, saboda samunsa da laifin yaudara, laifin da ya saɓa da sashe na 322 na kundin final cod.

Haka kuma, kotun ta umarci Malam Gambo ya biya surukar tasa naira miliyan biyu a matsayin diyya.