✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rukunin farko na daliban da Abba Gida-Gida ya dauka sun tafi karatu ketare

Daliban dai su ne rukunin na farko daga cikin dalibai 1001 da Gwamnatin ta dauki nauyin karatun nasu.

Kimanin dalibai 150 da Gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun digirinsu na biyu sun bar jihar a safiyar yau Juma’a don fara karatunsu a jami’o’in kasashen waje daban-daban wadanda suka hada da kasar India da Uganda wadanda kuma ake sa rai za su sami kwarewa a fannonin ilimi daban-daban.

Daliban dai su ne rukunin na farko daga cikin dalibai 1001 da Gwamnatin ta dauki nauyin karatun nasu.

Da yake jawabi game da muhimmancin shirin na tura dalibai kasashen waje, Gwamn Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa shirin wanda tsohon Gwamnan Kano, Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya kirkiro shi ya zama gata ga ’ya’yan Jihar don haka gwamnatinsa ta ga dacewar ci gaba da aiwatar da shi.

Gwamnan ya bayyana cewa a bayyane yake a fili yadda wadanda suka ci moriyar shirin a baya sune ke rike da manyan mukamai a cikin gwamnatinsa.

“Wannan aiki da ya yi yana tura dalibai kasashe waje ya haifar da samun kwararru a fannoni daban-daban a jihar daga cikinsu akwai irinsu Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi da Dokta Yusuf Kofar Mata da Farfesa Aliyu Isa Aliyu da kuma Mai ba Gwamnan shawara kan kirkire-kirkire, Bashir Muzakkar da sauransu.

Ana iya tuna cewa, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya gudanar da wannan shirin sau uku a wa’adin mulkinsa na biyu, inda ya tura dalibai kasashe kusan 16 a fadin duniya.

A jawabinsa, Kwankwaso ya yaba wa Gwamnatin Jihar bisa ci gaba da ta yi da wadannan ayyuka na alheri.

Ya yi kira ga daliban da su mayar da hankali kan abin da ya kai su don zama masu amfani ga iyayensu da kuma al’ummar jihar da kasa gaba daya.

Daya daga cikin daliban mai suna Babangida Salisu daga Karamar Hukumar Tarauni ya yaba wa Gwamnatin Abba wajen yin wannan kokari na tura su kasashen waje inda ya dauki alkawarin yin duk abin da ya kamata don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.