✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu da daure mai luwadi da kananan yara a jihar Sakkwato

Bana ba su komai, ina neman su ne in sun yi bacci, kuma ba a lokaci daya ba.

Wata babbar kota a jihar Sakkwato ta yi wa wani mutum, Lawali Bala daurin shekara 5 bisa laifin yin luwadi da kananan yara, a kauyen Rikina na karamar Hukumar Dange Shuni da ke jihar.

Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya (NAPTIP), ta gurfanar da shi a kan zargin laifuka da suka hada yaudara da zakkewa yara ta dubura.

Lawali bai yi gardama ba yayin da aka karanta masa laifukan da ake zarginsa da su inda ya nemi kotu ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun Isa Bargaja, ya yanke Lawali hukuncin dauri na shekara biyar a gidan kaso ya kuma ba shi zabin biyan tara ta Naira 50,000.

Aminiya ta ruwaito cewar Lawali dan asalin Karamar Hukumar Anka ne ta Jihar Zamfara, kuma ya shafe tsawon shekara biyu yana lalata da kananan yara.

Lawali ya bayyana wa wakilin mu cewar ya koyi mummunar dabi`ar ne
wurin abokansa labureri a jihar Neja, kuma tun daga lokacin ya kasa bari.

Ya kuma bayyana cewa yana neman yaran ne bayan dare ya raba idan sun yi bacci.

“Bana ba su komai, ina neman su ne idan sun yi bacci, kuma ba a lokaci
daya ba, idan na yi da daya yau sai in bari sai bayan mako daya in
kara yi wa wani,” inji shi.

An ruwaito cewa asirinsa ya tonu ne bayan damuwa ta sanya daya daga cikin yaran ya sanar da mahaifinsu, lamarin da ya sa mutanen gari suka tasa keyarsa har gaban ‘yan Hisba kuma aka gurfanar da shi a gaban Kuliya.