✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu da daure dan kasar China kan yaga kudin Najeriya

Kotu ta ci shi taraar N2,000 kan laifin yaga N3,000

Kotu ta yanke wa wani dan kasar China hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari kan wulakanta takardun kudin Najeriya, Naira.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta yanke wa dan kasar Chinan mai suna Li Lei Lei hukuncin ne bayan kama shi da laifin wulakanta kudin Najeriya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a I. Nicholas Oweiboo ya yanke hukuncin ne bayan hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Li bisa zargin aikata laifuka hudu da suka sabawa sashi na 21 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN).

Li Lei Lei ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa a lokacin da aka gurfanar da shi a ranar Tatala, 31 ga watan Mayu, 2022.

Daga nan sai alkalin ya yanke mshin hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu ko kuma biyan tarar Naira dubu dari biyu.

Abin da ya faru

Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ne dai suka kama Mista Li a ranar 17 ga watan Mayu, 2022 a lokacin da yake kokarin hawa jirgi zuwa kasar Kenya.

A yayin da jami’an suke binciken miyagun kwayoyi a jakar matafiyin ne ya fusata ya yaga wasu kudaden Najeriya, kimanin Naira dubu uku da dari biyu.

A dalilin haka ne jami’an suka kama shi suka mika wa jami’an tsaro na farin kaya, DSS.