Kasar Koriya, ta hannun Hukumar Agajin ta mai suna (KOICA) ta bai wa ma’aikatan Najeriya kyautar amawali domin hana yaduwar cutar COVID-19.
Shugaban makarantar ma’aikatan Najeriya, Abdul-Ganiyu Obatoyinbo ya karbi kayan da aka kawo, kamar yadda yake kumshe a takardar da hukumar ta fitar ranar Laraba.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban KOICA na Najeria Mista Woochan Chang, ya ce sun yi hakan ne domin taimaka wa yaki da cutar da kuma taimaka wa abokan huldarsu a lokacin tsananin da ake ciki.
Mista Woochan ya ce, agajin ya zo a lokacin da ya dace domin taimakawa a ranar amawali ta duniya da kuma gangamin #MaskOnNaija na ba wa mutane kwarin gwiwar yin da amawalin don kariya daga COVID-19.
Shugaban makarantar ya gode wa hukumar da daukin, tare da cewa takunkumin zai taimaka sosai wajen hana yaduwar annobar.