Kasar Koriya ta harba makami mai linzami na biyu a cikin kasa da mako guda a yayin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin yin zama kan gwajin wani makami mai linzami na farkon da ta yi a cikin makon.
A yayin da ake ci gada da yi wa juna kallon hadarin kaji tsakaninta da makwabciyarta, Koriya ta Kudu, a safiyar Talata ce hukumomin sojin Koriya ta Kudu suka ce Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami mai ’ya’ya zuwa cikin teku, kasa da mako guda bayan ta yi wani gwajin makami mai linzami da ya jawo ce-ce-ku-ce.
- Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami na farko a 2022
- Takarar Tinubu: Shugaba Buhari “ya shiga tsaka mai wuya”
- Najeriya A Yau: Yadda Rage Kwanakin Zuwa Makaranta Zai Shafi Dalibai A Kaduna
Majalisar Tsaron Koriya ta Kudu ta bayyana takaicinta game da harba makamin da Koriya ta Arewar ta yi, a yayin da Fira Ministan Japan, Fumio Kishida, ya ce, “Babban abin takaici ne yadda Koriya ta Arewa take ci gaba da harba makamai masu linzami.”
Ya ce, “Makami mai linzamain da Koriya ta Arewar ta harba ya yi tafiyar akalla kilomita 700 a sararin samaniya kafin ya fadi a gefen yankin da Japan ke iko da shi.”
Sai dai mai magana da yawun gwamnatin Japan, Hirokazu Matsuno, ya ce ba a samu bayanin ko makamin ya yi illa ga jiragen kasarsa ba tukuna.
Manyan Hafsoshin Tsaron Koriya ta Kudu dai sun ce an harba makamin ne daga kan tudu zuwa cikin tekun Japan daga Koriya ta Arewa.
Taron Kwamitin Tsaron MDD
Harba makamin na zuwa ne a yayin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin yin zama kan gwajin makami mai linzami mai gudun walkiya da Koriya ta Arewar ta yi a makon iya — Koriya ta Kudu dai ta bayyana tababarta a kan gwajin makamin da makwabciyar tata ta ke ikirari.
Koriya ta Arewa ta yi hakan ne bayan kasashe shida, ciki har da Amurka da Japan, sun bukace ta da ta guji yin “abubuwan da ke iya tayar da hankula” gabanin taron sirrin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar.
Kasashen Faransa, Birtaniya, Ireland da Albaniya su ma sun yi kira a gare ta cewa ta “shiga tattaunawa mai ma’ana game da manufarmu ta kawar da makaman nukiliya a ban kasa”.
Siyasar gwajin makamai
Masu sharhi dai na ganin kasar tana harba makaman ne domin ya zo daidai ta taron sirrin na Majalsiasr Dinkin Duniya.
“Koriya ta Arewa na ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya ne domin inganta su, amma a wannan karon ta tsara shi ne domin ya zo daidai da taron don cim-ma manufar siysasa,” kamar yadda Shin Beom-chul, daga Cibiyar Bincike da Dabarun Koriya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Wani mai sharhi kuma malami a Jami’ar Ewha da ke Seout a kasar Koriya ta Kudu, Farfesa Park Won-gon, ya ce akwai alamun ana gwajin makaman ne gabanin gasar wasannin Olympic na hunturu da aka shirya gudanarwa a birnin Beijing na kasar China a watan Fabrairu.
Idan ba a manta ba, an haramta wa Koriya ta Arewa shiga gasar saboda ta kaurace wa makamanciyar gasar da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan saboda COVID-19.
A halin yanzu dai kasar na zargin masu hana ruwa gudu da hannu a matakin da aka dauka a kanta a gasar na Beijing da ke tafe.