✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa na fuskantar barazana kan gwajin makami mai linzami

An haramta wa Koriya ta Arewa duk wani gwajin makami mai linzami da makaman nukiliya.

Amurka ta bukaci manyan kasashen duniya da su kakaba wa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri a sakamakon kasassabar da Pyongyang ta yi na harba makami mai linzami.

Gwajin da Koriya ta Arewan ta gudanar a ranar Alhamis da ta gabata, ya kasance karo na farko da take harba makami mai karfin gaske tun bayan wanda tayi a shekarar 2017.

Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa wannan mataki ya yi matukar harzuka manyan kasashen na duniya tare da kiraye-kirayen a ladabtar da kasar.

Kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya haramta wa Koriya ta Arewa duk wani gwajin makami mai linzami da makaman nukiliya baya ga sanya takunkumi kan shirye-shiryenta na kera makaman da aka ce nada hadarin gaske ga duniya baki daya.