Amurka ta ce alamu na nuna cewar kasar Koriya ta Arewa ta mallaki tarin makaman da ba a san adadinsu ba, bayan gwajin wani makami mai linzami mafi girma da Koriya ta Arewa ta yi a ranar Alhamis.
Mai Bai Wa Shugaban Amurka Shawara Kan Tsaro, Jake Sullivan, ya shaida wa manema labarai cewa matakin na Koriya ta Arewa wani yunkuri ne na takalar rigima, kuma suna zargin tana na da tarin makaman da ba a san adadinsu ba.
- Tsohon Fira ministan Togo ya zama shugaban kungiyar kwadago ta duniya
- Harin ’yan tawayen Yemen ya yi barna a rumbun ajiye man Saudiyya a Jeddah
Gwajin da Koriya ta Arewa ta gudanar shi ne irinsa na farko da ta yi a karkashin jagorancin Shugaba Kim Jong Un tun daga 2017.
Kamfanin dillancin labaran Koriya ya rawaito cewa, a karkashin sanya idon Shugaba Kim aka gwada makamin wanda yake tabbatar da aniyar kasar ta fuskantar duk wata kasa da za ta kalubalance ta.
Rahotanni sun ce sabon makamin ya yi tafiyar da ya zarce duk wasu makamai masu linzamin da aka gwada a shekarun baya tare da wani da aka kera na musamman domin kai hari ko’ina a cikin Amurka.
Tuni dai Amurka ta fara hangen gwajin makamin a matsayin wata babbar barazana, duba da irin takun sakar da ya jima tsakaninta Amurka da Koriya ta Arewa.