Kungiyar Ma’aikatan Gas da Man Fetur ta Najeriya (NUPENG) ta soki korar ma’aikatan kwantaragi 175 da kamfani hakar mai na Chevron Nigeria Limited ya yi.
Chevron ya sallami ma’aikatan da ke karkashin kamfanin da ke kula da ayyukan ofisoshi da leburanci na YKISH Integrated Services ne saboda sun shiga kungiyar NUPENG.
“Wannan abun bakin ciki ne da rashin imani wajen hulda da ma’aikata a lokacin da Mike ciki” inji takardar da kungiyar ta fitar.
Takardar mai dauke da sa hannun Shugabannin kungiyar na kasa, Kwamred Williams Akporeha da Kwamaret Olawale Afolabi, ta ce abin da kamfaninin cin zarafin ma’aikata ne.
Ta kuma ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a kamfanin da Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timipre Sylva, da su gargadi Chevron kafin kungiyar ta dauki matakin shiga yaji aiki.
NUPENG ta kuma ba kamfanonin kwana bakwai su gaggauta maido ma’aikatan bakin aikinsu.