✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kolo Toure ya zama sabon kocin Wigan Athletic

Ya rattaba hannun shekara uku da rabi a kungiyar.

Tsohon dan wasan bayan Arsenal da Kasar Ivory Coast, Kolo Toure ya zama sabon mai horar da kungiyar Wigan Athletic.

Wigan Athletic ta dauki Kolo Toure a matsayin sabon manajan ta domin maye gurbin Leam Richardson wanda ya kawo karshen aikinsa.

Toure mai shekaru 41 ya rattaba hannu akan kwangilar shekaru 3 da rabi, abinda ya kawo karshen aikin taimakawa Brendan Rodgers, manajan kungiyar Leicester City tun daga shekarar 2019.

Kolo Toure ya murza leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Manchester City, Celtic da sauransu.

Ya fara aikin horar da ‘yan wasa tun bayan da ya yi ritaya daga murza kwallon kafa.

Tsohon ‘dan wasan Cote d’Ivoire, Toure ya dade yana aiki tare da Rodgers wanda ya horas da shi a kungiyoyin Liverpool da Celtic, kafin ya dauke shi a matsayin mai taimaka masa.

Kolo Toure wanda ke cikin tawagar ‘yan wasan Arsenal da suka kafa tarihi kammala kakar wasanni ba tare da barar da wasa koda guda ba, ya ce darussan da ya samu lokacin da yake aiki tare da Rodgers za su taimaka masa wajen sauke nauyin aikin da aka dora masa a Wigan.

Toure ya bayyana matukar farin cikinsa da nadin da aka masa, lura da cewar Wigan ba karamar kungiya ba ce da ke da dimbin magoya bayan da yake sa ran su taimaka masa wajen samun nasara.