✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kokawa Da Gwamnatin Buhari: Martani (3)

Hafiz Koza Adamu: Alal hakika ba wanda zai ja cewa a wannan gwamnati, ‘An yi saka da mugun zare.’ Hatta Uwargidan Shugaban kasa Buhari ta…

Hafiz Koza Adamu: Alal hakika ba wanda zai ja cewa a wannan gwamnati, ‘An yi saka da mugun zare.’ Hatta Uwargidan Shugaban kasa Buhari ta fahimci hakan, ta kuma bayyana. A wancan lokacin an yi ta ce-ce-ku-ce a kan maganar da ta yi, sai dai yanzu duk mai idanu da zuciyar gaskiya ya san abin da ta fadi sai aukuwa yake.

Idan aka koma ga batun cin hanci da rashawa kuma, to idan ma an samu canji, bai fara bayyana ba. A nan ma duk wanda ya kwana, ya wuni, a Najeriya ya sani ko kuma yana ganin yadda wannan kazamar harkalla ke ci gaba da bunkasa, kamar ba gobe!

Lallai Boko Haram tafiya ta mika, to amma fa in dai har mahara na iya cin taryen tawagar gwamnan babbar jiha a kasa kamar Najeriya, har a yi dauki ba dadi, to matsalar tsaron da ake tunanin ta kau, gaskiya da sauran rina a kaba.

Abin da ya kamata dai shi ne, a fito a fadi gaskiya, a bayyana wuraren da gwamnati ta yi kuskure, a kuma fadi hanyoyin gyara, kamar yadda Malam ke yi. Allah Ya sani idan duk al’ummar da ya kamata su fadi a ji, suka ja baki suka yi gum, to an shiga hakkin talakawa, marasa amon kai wa ko’ina.

Gyara kayanka, ba sauke mu raba ne ba!

Umar Alkasim Idris: Lallai wannan gwamnati ta yi kokari musamma kan murkushe ‘Yan Neja-Delta da Boko Haram da sauran su, amma maganar cin-hanci da rub-da-ciki da wawaso bai canza ba. Kodayake ya canza riga ko in ce salo,wato yanzu suna sara ne suna kallon bakin gatari, ta hanyar da idan aka nuna to tsoho zai leka, ko in ce magu na nan ya yi zaman ‘yan caca.

Yuseef Yahaya Gumel: Mun karanta, mun ji, mun gani, mun fahimta sai dai da sauran rina a kaba a jagorancin kasar nan muddin ba tashi tsaye aka yi ba akwai yiwuwar yau ta koma jiya. Ba ma fatan haka amma muna da bukatar canji.

Danladi Haruna: Zatona fa sun yi karatun ta nutsu tun farko. Matsalar kafin su biya allon suka wanke suka soma rubuta alu ambaki

Muhammad Bashir Abdallah: Kowane mugu yana zuwa da irin salon muguntarsa ne. Akwai masana da manazarta a cikin wannan kasa, bai dace su zura ido ba kasarmu ta koma kamar gandun dabbobi.

Allah ya saka maku da alkairi Farfesa bisa wannan kokari da kuke yi. Al’ummar kasar nan tana kishirwa mutane irin ku.

Mafitar kasar nan tana hannun masu ilimi ne wadanda ke kishin al’ummarsu. Bai kyautu a ce ku bar jahilai suna ci gaba da jahilci a cikin kasa da sunan shugabanni ba. Ya kamata da ku da ire-irenku ku yi wani abu. Ko ba komai, ‘ya’ya da jikoki da tattaba-kunne da umhuhun suna tafe. Ya kamata mu yi wani abu da za su gani su ce Allah ya saka wa su baba da alheri da suka kona kansu don sama mana haske. Allah Ya taimaka.

Abubakar Hassan: Malam Allah Ubangiji Ya saka da alheri da wannan sharhi mai cike da fadakarwa. Don kuwa, in dai masana irinku za su ci gaba da zura wa wannan gwamnati idanu, to lallai za su kai mu su baro.

A lokacin zamanin Jonathan mun zarge shi da rashin kwaba wa duk wanda ya rub-da-ciki da dukiyar al’umma. To a lokacin gwamnati mai ci, sai ya zamana wadanda ba ‘yan jam’iyya ba ne kawai ake iya kwaba. Ina batun Babachir da Abba Kyari da sauran su. A can baya mun zargi Jonathan da bai wa jami’an gwamnati kusan kashi saba’in ko tamanin a lokacin cike wasu guraben ma’aikta ko sababbi, amma a yau bayan mun zabi canji sai ya zama wannan gwamnati tana ba jami’anta kashi dari bisa dari.

To Lallai in muka ci gaba da irin wannna makauniyar tafiya, lallai za a kai inda al’umma za su ce gara jiya da yau. Da fatar ba za mu tsinci kanmu cikin wannan yanayi ba.

Sulaiman Aliyu Zango: Fatata Maiduka ya kalli dumuiniyar Farfesa, na kokarin haska mana hanya don fitowa daga kwatamin da muka fada.

Ko shakka babu tsintsiya ta share dakinta sarai na kazantar da ke rikidewa ta zama cuta mai yi wa duk wanda ta kama dauka daya. Duk da cewa akwai wasu kwazazzabai nan-da-can, amma ya kamata a ce, idan an bi ta barawo to fa a bi ta mai kaya. ‘Yan kasa sun kira canji a baki amma halayensu da ayyukansu ba su shirya daukar canjin ba ta kowace irin fuska. Misali, idan ka dauki ‘yan kasuwa har yanzu tauye ma’auni yana nan ga wasu ‘yan kasuwarmu. kalular zuwa ofis tana nan ga wasu ma’aikatanmu. Malaman makaranta da dalibai kowa neman sa’ar kowa yake ya kwantar da shi. Magidanta na limancin gidansu ido rufe.

Kai! Hatta mai tukin mota ba ya duba hakkin mai babur, haka shi ma idan ya samu mai keke sai ka ga ya murkushe shi balle mai tafiya a kafa wanda suna ganin bai kamata ya hau titi ya mori romon damukuradiyya ba.

Duk wannan rashi tausayi da son kai namu ‘yan Najeriya ‘Limamin Canji muke jira ya canza mu’. Mazaunan kowa cikin takawan damfare yake da kashi amma kowa ba ya jin warin nasa sai na dan uwansa, kuma duk kowa na jiran mutum daya ya zo ya wanke ma kowa. Anya kuwa zai iya fitar da warin kashin can?

Muhammad Suleiman: Mu dai ‘yan Najeriya masu raunin gata, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen neman agajin Allah Madaukakin Sarki ya ceto mu daga kangin mulkin ‘yan jari hujja.

Inuwa Sai’du: Wannan gaskiya ne Farfesa. Hakika yau kasar nan tana cikin wani hali, musamman ma a jiha ta Jigawa. Saboda mu ba ‘ya ‘yan wasu ba ne aka kira mu jarabawa da azumin Allah, aka tantance mu, sai daga baya bayan jarabawa ta fito, wai ba a son masu irin karatunmu, sai shafaffu da mai. Akwai Allah!.

Rabi’u Falalu Zango: Gaskiya da rakumi zai bi akala da ba a samu tangarda wajen tafiya ba, amma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai yi tsiya (fashewa).

Isah Halliru: Kukan kurciya jawabi ne mai hankali shi ke ganewa. Allah Ya sa wadanda aka yi domin su, sun ji. Farfesa Allah Ya saka da alheri.

Mun kammala