Umar Alkasim Idris: Ina kyautata zaton wannan mulki ya zo ne da kyakkyawar manufa, musamman a mataki na shugabancin kasa, amma sai dai kash! an yi kitso ne da kwarkwata a ciki. Duk da masu iya magana kan ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai, to ai ya kamata a yi dambun daidai da masu ci, yadda ba za a ci, a rage, a zubar ba. Mun gode da fashin baki.
Khalid Prince Arkam: Gaskiya ne wannan magana. Da za su yi amfani da wannan shawara, da sun samu mafita, amma muna yi musu addu’a Allah Ya kawo masu mafita. Allah ya kara wa Malam lafiya da kaifin basira, ya rika tunatar da mu da shugabanninmu, amin.
Lawal Sani Soba: Allah ya taimaki Farfesa, wato akwai ofisoshin wadansu daga cikin zaba-u da kuma na nadi wadanda ba su san aikinsu ba.
Hujja ita ce, idan an zabi mutum a matsayin wakili, wannan wakilin hakkinsa ne ya san duk matsalolin da ke faruwa a inda yake wakilta. Idan ya tattara matsalolin, sai ya garzaya majalisa da su domin a tattauna.
Bugu-da-kari, idan al’umma suka kai koke ga mai wakiltar su, sai su buge da ba su cin hanci (kudi).
Shugaba, idan ya aikata abin da ba daidai ba, wakilanmu ba su iya tsawatar da kuma dakatar da shi. Hasali ma, shugaba kan bai wa wakilan al’umma cin hanci domin ya aikata abin da yake so. A wata fuskar kuma, shugaba kan dauki masu ba shi shawara, amma duk wanda aka bai wa wannan matsayin to tasa biyayya ce kawai. Haka kuma mai-bada-shawara, na kallon barna, amma haka nan zai ce ‘ka yi daidai ranka-ya-dade’. Ke nan shawarar bogi ake bayar wa.
Daga karshe, idan aka samu tsayayyun wakilai, suka yi wakilcin kwarai, to shugabanci a kasar nan zai yi dadi. Domin kuwa ni a ganina, duk matsalolin Najeriya ya ta’allaka ne a wajen masu wakiltarmu.
Sanusi M. Ladan Kebbe: Ya yi daidai. Mafi yawancin mutanen kasar nan suna ta’allaka matsalolin kasar nan ko kuma rashin magance su ga shugaba Buhari kawai. Sun manta da masu hana-ruwa-gudu, wato ‘yan majalisa da kuma bangaren shari’a. Idan masu wakilta suka kasance komai ya fito a aljihunsu, to me shugaba zai yi? Yau bangaren zartarwa ba ya da ikon ya yi ganin damar sa a abubuwan da suka dami talakawa ba tare da shawartar majalisa ba. Su kuma sun zama ramin kura. Dole ne a ga al’amurra na tafiyar hawainiya. Haka mafi yawancin ‘yan majalisun ko dai ‘yan adawa ko kuma angulu-da-kan-zabo. Sun shigo jam’iyya ne kawai domin su bi wannan guguwar su ci zabe, kuma manufar su daban. Mutane sun san zaluncin da suka yi a da, amma aka bar su suka sake tsunduma a gwamnati. Idan zalunci ya yi rinjaye a kasa, ina ake tsammanin saurin samun cigaba, an bar mutum daya da kashin mahaukacin kare? Har yanzu mutane ya kamata su tashi tsaye su sake ba shugaba Buhari dama tare da tabbatar da cewa sun rage masa aiki da azzalumai. Yanzu ko gwamnoni, an manta da su ne? Me ye anfanin su duk da kudaden da ake ba su na su yi amfani da su su rage wa mutanen yankunansu radadin talaucin da ke damun su? Mutane su daina fakewa da guzuma suna harbin karsana, ko kuma abin da ake cewa barin jaki ana dukan taiki.
Moh’d Yusuf Moh’d: Lallai kam ya kamata ai duba na tsanaki a kan gudanar da wannan shugabnci da kyau. korafe-korafan da ake a kan wasu mutane na cewar sun kankane sun hana ruwa gudu abin dubawa ne. Na ‘yan uwa da ‘ya’yan abokan arziki a kan mukamai na daga cikin abin da ke jawo korafe-korafe na cewar suna cin karensu babu babbaka, shi ma abin dubawa ne. Wanda suka yi fafutika wajan tabbatar da nasarar kafuwar gwamnatin suke korafin an yada su, an dauko wasu aka ba su mukamai a wannan gwamnati su ma abin dubawa ne. Talakawa da suka jajirce wajan tabbatar da kafuwar gwamnatin duk korafinsu, shi ma abin dubawa ne. Duk wani shiri na gwamnati da zai jawo wa talakawa wahala da kuncin rayuwa abin dubawa ne.
Muhammad Bashir Abdallah: Duk abin da son rai da ninanci suka zamo abokan tafiyarsa, to lallai wannan tafiya takan zamo kwan-gaba-kwan-baya.
Sau da yawa mutum kan so abu, amma abin nan ya zamo sharri ne a gare sa. Haka kuma mutum kan nuna kiyayya ga abu, alhali abin nan, alheri ne a gare.
Mu dai yi tunanin ta natsu,domin mu samar wa kanmu da kanmu mafita, don na ji an ce “Allah Ba Ya Canzawa Da Kansa, Sai In Mutane Sun Canza”
Allah Ya yi mana muwafaka!
Lawal Ibahim Tanimu: Akwai abin lura. A ganina, gwagwarmayar amsar mulki kawai aka sa a gaba, amma babu wani ingantaccen tsari don samar wa Najeriyawa sauki dangane da kuncin rayuwar da suke fama da shi. Bayan kuma mulkin ya samu, sai aka rasa hannun kwarai a cikin mafi yawan mataimaka ko mashawarta da sauran mukarrabai. Sai kawai abin ya zamo tamkar ja-ya-fado-ja-ya-dauka. Maimakon saukin da Najeriyawa ke tsammani, sai kawai suka dada tsunduma a cikin taskun da kusan a ce gara jiya da yau. Allah Ya kyauta.
Abdulkadir Zailani: Allah Ya kyauta, domin wannan magana da ka yi sai mashirmanta su fara zargin ka da cewa kai dan wata jam’iyya ce alhali gaskiyar zance kake bayyanawa. Allah Ya biya.
Umar Jajere Muhammad: Ai kowa ya samu rana dole ya yi shanya. Duk mazaunin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Bauchi da Neja, da Abuja da uwa-uba Kano, in dan halal ne shi dole ya yaba wa wannan gwamnatin. Mu dai mun yaba.
Aliyu Mangwabsa: Kafin a ci gaba da wannan rubutu domin na ga kashi na daya ne, ya kamata mai rubutu ya yi shimfida kyakkyawa dangane da sharhin da yake yi. Na farko, yana da kyau a nuna karara halin da kasar take ciki a lokacin da gwamnatin canji ta karbi mulki. Duk wasu alkalumma na bayanan ci gaban dan Adam ya sani sai a kawo su.
Za Mu Ci Gaba