A bisa wani roko na musamman daga Qatar, gwamnatin Turkiyya ta mika wa majalisar kasar bukatar aika sojojinta domin bayar da tsaro.
Majalisar kasar Turkiyya ta amince da wata bukata da gwamnatin kasar ta kai domin amincewa na aika da sojoji zuwa Qatar a watan Nuwamba domin inganta tsaro a lokacin Gasar Kofin Duniya da za a yi a kasar.
- Gasar Kofin Duniya: Qatar ta rage lokacin aiki da makarantu
- FIFA ta dakatar da Rasha daga buga kofin duniya na 2022
Gwamnatin ta shigar da bukatar amincewar ne a bisa rokon kasar Qatar na yin hakan a makon nan.
A cewar Qatar, cikin wata takardar da ta aika wa Turkiyya, “Bukatar kai sojojin wani mataki ne na dakile duk wata barazana, musamman ta ta’addanci a lokacin gudanar da gasar ta kasa da kasa”.
Sojojin za su kasance a Qatar ne tsawon wata shida, a yayin zamansu, za su bayar da tsaro a lokacin gasar, amma a karkashin umarnin mahukuntar kasar.
Baya ga Turkiyya, ana sa rai Kasashen Amurka da Faransa da Britaniya da Itali da kuma Pakistan za su bayar da ta su gudunmawar sojin domin gasar.