An kwace kwalaben magananin tari na Kodin na ruwa guda dubu dari da aka yi fasakwaurinsu, kafin shigarsu kasuwanni a Najeriya.
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama muggan kwayoyin ne a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne da ke Jihar Ribas.
- Mutum 93 ’yan bindiga suka kashe a kauyen Zamfara
- Zamfara: An dakatar da Sarkin Zurmi kan ayyukan ’yan bindiga
- NDLEA ta kwace Tiramol kwaya miliyan 5 a tashar jirgi
Jami’in Hulda da Jama’a na NDLEA na Kasa, Femi Babafemi ya ce masu fasakwaurin sun sanya Kodin din ne a cikin kwalayen kayan abinci domin bad-da-kama; Amma Hukumar ta gano.
Ya ce an gano bad-da-bamin da aka yi wa miyagun kwayoyin ne a yayin binciken hadin gwiwar NDLEA da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), da Hukumar Kwastam, da kuma Hukumar Tsaro ta DSS a tashar jirgin ruwan.
Amma jami’in ya bayyana cewa, “Har yanzu babu wanda ya fito ya ce kayan nasa ne, amma muna kokarin bin diddigi mu gano wanda ya shigo da su, ya fuskanci hukunci.”
Babafemi ya ce, NDLE ta kuma kama ganyen kara kuzari na ‘khat’ mai nauyin kilogram 146.9 da aka yi fasakwaurin sa zuwa Najeriya a filin jiragen sama na Abuja.
Da yake yaba wa hukumomin kan kamen, Shugaban NDLEA na Kasa, Buba Marwa, ya ce, “Da kwalaban Kodin din guda 100,000 sun kai ga hannun matasa a kauyuka da biranenmu, to da barnar da barnar da za su yi ba za ta misaltu ba;
“Haka shi ma kilogram 146.95 na ‘khat’ din da ya samu sulalewa zuwa cikin al’umma.
“Amma jami’anmu za su ci gaba da yin iya kokarinsu tare da sauran masu rauwa da tsaki wajen yaki da miyagun kwayoyi,” inji shi yana mai jinjina game da nasarar kama miyagun kwayoyin da aka yi.