✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kocin Real Madrid Zidane ya kamu da Coronavirus

Sanarwar kamuwarsa ya fito ne a ranar juma'a daga shafin kungiyar Real Madrid.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya harbu da cutar Corona.

Labarin kamuwarsa da cutar ya bayyana ne ranar juma’a, lokacin da yake kokarin ganawa da manema labarai gabannin karawar Real Madrid da Alaves a karshen mako.

Mataimakinsa David Bettoni, zai ci gaba da jan ragamar Real Madrid har zuwa lokacin da Zidane din zai warke.

Kungiyoyin da Real Madrid za ta buga wasa da su nan gaba su ne; Alaves, Levante, Huesca da kuma Getafe.

David Bettoni, mataimakin Zidane, ya ce kocin na ci gaba da warwarewa, bayan killace kansa da ya yi, kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Laliga ta tanadar.