✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Kocin Najeriya Amunike ya bayyana sunayen ’yan kwallonsa

Kocin kungiyar kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) Emmanuel Amunike ya bayyana sunayen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a…

Kocin kungiyar kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) Emmanuel Amunike ya bayyana sunayen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a gasar cin kofin duniya na matasa na ’yan kasa da shekara 17 da za a fara a gobe Asabar a kasar Chile.
Kocin ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin da ta wuce jim kadan bayan ya bayyana sunayen ’yan kwallon cewa, ya yi imani ’yan kwallon da ya zakulo don su kare martabar Najeriya a gasar za su ba marada kunya.  “Na yarda da ’yan kwallon da na zaba kuma na tabbata za su ba marada kunya a gasar cin kofin duniya da Najeriya za ta kare kambunta a Chile, kuma abin da kawai muke bukata shi ne magoya bayanmu su yi mana addu’ar fatar samun nasara a gasar”, inji shi.
Daga cikin ’yan kwallon da kocin ya gayyato sun hada da:  A bangaren masu tsaron gida (Goalkeepers) akwai: Akpan Udoh da Amos Benjamin da kuma Chison Chiaha.  A bangaren masu tsaron baya (Defenders) kuma akwai Tochukwu Ibe, da Lukman Zakari da Ejike Ikwu da kuma John Lazarus. ’Yan kwallon tsakiya (midfielders) sun hada da Dabid Enogela da Kingsley Micheal da Samuel Chukwueze da Edidiong Essien da Chukwudi Agor da Joel Osikel da Kelechi Nwakali da kuma Chinedu Madueke.
A bangaren ’yan kwallon gaba (Forwards) kuwa kocin ya gayyato Funsho Bambgoye da bictor Osinhen da Sunday Alimi da Odochukwu Ammudu da Orji Okonkwo da kuma Osinachi Ebere.
Najeriya dai za ta fafata ne a rukunin A da kasashen Chile da Croatia da kuma Amurka.