Kocin kasar Libya Adel Amrouche a ranar Litinin da ta wuce ya fito fili ya nemi gafarar ’yan Najeriya bisa wata katobara da ya yi, inda ya ce Najeriya tana amfani ne da tsafi wajen yin nasara a duk wasannin da take yi, yayin da kasar Libya kuma ta dogara da Allah.
Libya dai tana rukuni daya ne da Najeriya a wasan neman zuwa Gasar cin Kofin Afirka da za a yi a Kamaru a shekara mai zuwa. Kuma kawo yanzu Libya ce take saman teburin da maki 4 sai Afirka ta Kudu ta biyu da maki hudu sai Najeriya ta uku da maki 3 sai Seychelles ta karshe wadda ba ta da maki ko daya.
Najeriya dai za ta hadu da Libya ne a wasa na gaba, wasan da ake ganin zai yi zafi, domin duk kasar da ta yi sake, to za ta ji a salansa.
Sai dai jim kadan bayan kocin ya furta kalamin ne sai ya rika samun suka daga ko’ina musamman daga wajen ’yan Najeriya.
Ganin haka ne ya sa kocin dan asalin Aljeriya mai shekara 50 ya shiga shafinsa na Twitter ya nemi gafarar ’yan Najeriya kuma ya ce Libya ba ta shakkar Najeriya a karawar da za su yi nan gaba.