Jim kadan bayan da kasar Uruguay ta fitar da Italiya a gasar cin kofin duniya a ranar Talatar da ta wuce ne Kocin Italiya mai suna Cesare Prandelli ya ajiye aiki.
Italiya dai ta kasa kai wa matakin zagaye na biyu a gasar ce bayan ta samu rashin nasara sau biyu a jere. A wasanta na farko Costa Rica ce ta yi mata lalata da ci daya mai ban haushi yayin da Uruguay kuma ta doke ta da ci daya mai ban haushi da hakan ta sa kasar ta gama da maki uku daga wasanni uku da ta yi. kasashen Costa-Rica da na Uruguay ne suka haye zagaye na biyu a gasar yayin da kasashen Italiya da na Ingila kuma suka koma gida.
Sau biyu ke nan a jere ake fitar da kasar a gasar cin kofin duniya tun a zagayen farko da hakan ta sa kocin yanke shawarar ajiye aiki.
Da ma ana gab da fara gasar ce kocin ya sabunta kwantaraginsa amma saboda rashin tabuka abin kirki ta sa shi yanke shawarar rabuwa da kwallon mangwaro don ya huta da kuda.
Kocin Italiya ya ajiye aiki
Jim kadan bayan da kasar Uruguay ta fitar da Italiya a gasar cin kofin duniya a ranar Talatar da ta wuce ne Kocin Italiya mai…