✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Ateletico Madrid ya sabunta kwantaraginsa

Kocin Atletico Madrid da ke Sifen Diego Simone ya sabunta kwantaraginsa a kulob din kamar yadda wata sanarwa da kulob din ya fitar ta nuna…

Kocin Atletico Madrid da ke Sifen Diego Simone ya sabunta kwantaraginsa a kulob din kamar yadda wata sanarwa da kulob din ya fitar ta nuna a ranar Talatar da ta wuce.

Kocin ya sabunta kwantaraginsa ne daga yanzu har zuwa shekarar 2020 bayan ya shafe ranar Litinin yana kai kawo wajen ganin ya kulla yarejejniya da kulob din.
Da wannan sabunta kwantaragin da kocin ya yi, yanzu za a iya cewa ya kawo karshen rade-radin da ake yi na yiwuwar canza shekarsa zuwa wadansu kulob a Nahiyar Turai da ke zawarcinsa.
A Disambar 2011 ce kocin ya fara horar da kulob din Atletico Madrid bayan da kulob din ya sallami tsohon kocinsa Gregorio Manzano. Diego Simone ya samu nasarar lashe kofunan La-Liga da na Copa del Rey da Europa League da Supercopa de Espana da kuma UEFA Super. Sannan ya taimaka wa kulob din wajen hayewa wasan karshe a karon farko a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) inda ya sha kashi a wajen kulob din Madrid da ci 4-1 a bara.