✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko yanzu aka yi zaɓe Tinubu ne zai yi nasara — Oshiomhole

Babu wani ɗan siyasa a Nijeriya mafi shahara da sauye-sauyen sheƙa a tsakanin jam’iyyu kamar Atiku.

Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ko yau aka yi zaɓe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai yi nasara.

Oshiomhole wanda shi ne mai wakiltar shiyyar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a safiyar wannan Larabar.

Tsohon gwamnan na Jihar Edo ya faɗi hakan a lokacin da yake tsokaci kan sauya sheƙar da Sanatocin Kebbi uku suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Ya ce, Tinubu ya ɗauki ƙwararan matakai domin daidaita Nijeriya, yana mai cewa kafin gwamnatinsa manoma a wasu sassan ƙasar ba sa iya shiga gonakinsu amma yanzu lamarin ya sauya.

Da yake tsokaci kan guguwar sauyin sheƙa da ake gani a halin yanzu, Oshiomhole ya ce babu wani ɗan siyasa a Nijeriya mafi shahara da sauye-sauyen sheƙa a tsakanin jam’iyyu kamar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar.

“A yanzu babu wani ɗan siyasa a Nijeriya mafi dacewar rubuta littafi kan sauya sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa wannan kamar Atiku,” in ji Oshiomhole.

Ya yi bayanin cewa Atiku ya fi kowane ɗan siyasa shahara idan an taɓo batun sauya sheƙa domin a cewarsa shi ne ya fara ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa ACN wadda ta rikiɗe zuwa APC.