Majalisar Tarayyar Najeriya da ke Abuja ta rabu zuwa Majalisar Dattawa mai wakilai daga dukkan sassan kasar nan har 109 da Majalisar Wakilai mai wakilai ita ma daga dukkan sassan kasar har 360. Majalisar farko ita ce babba, ta biyun kuma ita ce karama. Majalisar Tarayya ita take da alhakin sa ido ga sauran rassan gwamnati guda biyu wato: reshen shari’a da yake dauke da alkalai da kotuna da kuma reshen zartarwa mai dauke da Shugaban kasa da ministoci da sauran nade-nadensa. Manufar sa idon majalisar ga wadannan rassa guda biyu shi ne don ganin cewa ba su karya wata doka ba daga cikin dokokin kasa yayin gudanar da ayyukansu, misali ga reshen shari’a a aikin su na hukunta masu laifi da aka gurfanar a gaban su da kuma yayin fassara doka. Haka zalika, ita dai wannan majalisa aikinta ne tsawatarwa ga shugaban kasa da ministoci da sauran nade-nadensa ya rataya, don tabbatar da cewa Shugaban kasa da mukarrabansa ba su karya wata doka ba yayin zartar da mulki ga ‘yan kasa, idan kuma sun karya majalisar ta tsige su daga mukamansu kama daga wadanda shugaban kasar ya nada har ma da shi kansa shugaban kasar! Wannan majalisar dai ita ce take da alhakin tantance da kuma tabbatar da ministoci da sauran nade-naden da shugaban kasa yake son yi don ganin cewa suna da nagartar da za su taya shugaban kasa aikin ciyar da kasa gaba bisa doka. Karya dokar kasa da rassan gwamnati suke yi shi ne yake dakile ci gaban kasa ya sanya talaka cikin halin ni ‘ya su. Uwa uba dai ita Majalisar Tarayyya “babban” aikinta shi ne yin doka ko yi wa dokar kwaskwarima domin “amfanar” da ‘yan kasa.
Duk dan Najeriya da ya mallaki hankalin sa ya san ayyukan da na zayyana a sama ba su ba ne ayyukan da ‘yan majalisun mu suke yi ba yanzu, domin na farko da yawa daga cikin su ta hanyar magudin zabe suka samu tikitin takara, kuma ta irin wannan hanyar suka samu nasarar lashe zabe, wasu lokutan bayan sun jikkata talakawa da asarar rayuka da ta dukiya. Sauran kuwa da ba ta magudi suka je majalisar ba, za ka samu cewa ba saboda ana son su aka zabe su ba, sai don sun sayi kuri’ar masu zabe. Duk da samun gindin zama da magudi ya yi ga ‘yan majalisun, ba a rasa na Allah da ba su yi magudin ba, amma sai dai ‘yan tsirari ne, sun yi karancin da za a iya cewa mai hankali ne kawai yake iya gane furfurar farar tunkiya! Yanzu ke nan da ba su da rigar kariya!
Aikin da ‘yan majalisu suka fi shahara da shi shi ne, yin cushe a cikin kasafin kudi da yin bita- da- kulli ga wadanda shugaban kasa ya nada a mukamai, kuma aikin su ya biyo ta kan ‘yan majalisun, da saya wa kansu motoci na biliyoyin Nairori da yin dokokin da za su biya musu bukatun kansu ba bukatun wadanda suka aika su majalisar ba da daukar albashi mai gwabin da ya saba wa hankali, saboda tsananin yawansa da daukar alawus-alawus shi ma mai gwabi irin na albashin. Hakan ne ya sa ma suke rasa abin da za su yi da kudi. Don haka sai su yi ta yin almubazaranci da kudin ta hanyar yin gasar sayen motoci na alfarma da yin dogayen gine-gine na kece raini da neman matan banza masu matukar tsada da bin bokaye, tare da ba su kyaututtukan miliyoyin Naira da gidaje da filaye da kuma kujerun hajji da umara zuwa kasashe masu tsarki na Saudiyya da na Jerusalam barkatai.
A daidai wannan lokacin da suke cin karensu ba babbaka kusan kashi 90 cikin 100 na wadanda suke wakilta suna mutuwa a kullum saboda yunwa ko saboda babu ‘yan daruruwan Naira da za su sayi magani ko saboda babu magunguna da kayan aiki wadatattu, kuma ingantattu a asibitoci ko saboda lalatattun tituna da suka fi kama da tarakunan mutuwa. Bugu da kari a daidai wannan lokacin da ‘yan majalisu suke sheke ayarsu, sojoji da ‘yan sanda suna ta mutuwa a kullum a sakamakon rashin kayan aiki wadatattu ingangattu, sannan kuma bayan sun yi asarar rayukansu a bakin fama, babu wani kulawa da iyalansu da suke bari ke samu tun da su kan su jami’an tsaron lokacin da suke raye ma kasa ke morarsu ba su samu kulawa ba. Wannan rikon sakainar kashin ga jami’an tsaron na daga cikin manyan dalilan rashin murkushe Boko Haram da tasagerun Neja Delta har yanzu!