Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda gwamnati ta amince Majalisar Dokoki ta Kasa ta kashe Naira biliyan 37 don gyara ginin majalisar, duk da kuncin rayuwa da talakawan Najeriya ke ciki a yanzu. Ga yadda suka bayyana ra’ayoyinsu, inda wadansu suka nuna rashin amincewarsu wadansu kuma suka amince a kashe kudin:
Gaskiya kudin ya yi yawa – Dauda Usman
Daga Aliyu Babankarfi, Zariya
A gaskiya kudin ya yi yawa lura da halin da kasa ke ciki a yanzu na kokarin farfado da tattalin arzikin kasa. Da a kashe kudin ta wannan bangaren gara a kashe su a yaki da Boko Haram da kuma yaki da barayin shanu, domin al’umma yankin su samu saukin rayuwa. Ai dama ginin majalisar a gyare yake nawa ra’ayin ke nan.
Sam bai dace ba– Halliru Hamza
Daga Aliyu Babankarfi, Zariya
Ni a ra’ayina bai dace ba a kashe har Naira biliyan 37 wajen gyara ginin majalisa, idan aka yi la’akari da irin halin talauci da rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan.
Kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da wannan kudi wajen kara tallafa wa hukumomin tsaro da inganta walwalar jama’a. Ya kamata gwamnati ta sani cewa, al’umma sun zura mata ido domin ganin an samu bambanci a tsakaninta da gwamnatocin baya.
Ya dace majalisa ta kashe kudin – Harira Chibra
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Ni Harira Aliyu Chibra, ina ganin ya dace ’yan majalisar nan su kashe wannan kudi domin lokacin siyasa ne a ciki ne za su samu nasu rabon su dawo yankunansu su taimaki jama’arsu. Ai kwangila ce ba kai-tsaye za a yi aikin ba, kuma ko kai-tsaye ne su yi mana ba lokaci daya ba ne, idan aka gyara ya wuce ai shi ke nan kowa ya san aikin kwaskwarimar gini ya fi sabo cin kudi.
Bai dace su kashe kudin ba – Babangida Mai Atamfa
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Gaskiya ni a ra’ayina bai dace ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa su kashe wannan dimbin kudi wajen gyara kawai ba, lura da yanayin da ake ciki na kunci rayuwa a kasar nan. Talakawa suna fama da rashin tsaro da rashin hanyoyi da sauransu ba a yi ba, a ce za a kashe makudan kudi har Naira biliyan 37, kudin sun zama daidai da wanda aka ware wa bangaren lafiya na kasar nan a kasafin kudi, wannan babu adalci a cikinsa.
Kamata ya yi a ce sun sake dubawa su tausaya wa halin da al’umma suke ciki, idan ya so daga baya idan abubuwa suka daidaita sai a gyara ginin majalisar. Amma yanzu a gyara al’ummar kasa tukunna.
Bai dace ba– Malam Bello Kaita
Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina
Yanayin da ake ciki a yanzu ba gyaran majalisa ba ne ya kamata a yi. Akwai matsalolin hanyoyi, asibitoci, makarantu, wutar lantarki ga batun tsaro da sauransu, su ne ya kamata a gyara ba wai ginin majalisa ba. Har ila yau, akwai batun gyaran noma wanda ya dace a duba. Duk wadannan matsaloli in aka yi amfani da wadannan kudi lallai za a samu ci gaba. Saboda haka, babu wata fa’ida a wannan gyara domin ba tsufa ta yi ba balle a ce ta lalace.
Ba ya da wani amfani – Alhaji Labaran Mai Nama
Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina
Babu dalilin fitar da wadannan kudi bayan ga mutane na mutuwa sai a ce su kadai ke ci? Ban ga amfanin gyaran ba. A bar ta kawai yadda take. A tafi a haka har wannan mulkin ya kare. Ai kamata ya yi su rika taimaka wa jama’a ya fi wannan gyara domin ba an zabe su don gyara majalisa ba. Da batun kayan aikin jami’an tsaro suka ce za su inganta da wadannan biliyoyi har addu’o’i sai sun samu. Amma a ce wai gyaran ginin majalisa, ba ma gina sabuwa ba, haba!