Gwamnatin Buhari ta yi shirin bayar da tallafin Naira dubu biyar a wata ga marasa aikin yi a Najeriya. Sai dai a makon jiya Majalisar Dattijai ta nuna kin amincewa da shirin. Abin tambaya a nan shi ne, shin hana wannan tallafin ya dace kuwa? Ga abin da mabambantan mutane suka bayyana a kan batun:
Tallafa wa matasa shi ne daidai – Muhammad Nuraddeen
Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna
Muhammad Nuraddeen: “A ra’ayina, a gaskiya matasa suna bukatar taimako ta kowane fanni daga wajen gwamnati. Don haka kin yarda da Sanatoci suka yi na a kin ba matasan tallafin Naira dubu 5 a kowane wata, yin haka bai dace ba. Ke nan kamar Sanatocin sun amince da cewa matasan su ci gaba da yin ayyukan ta’addanci ne a kasa tun da matashin da ba shi da aikin yi tamkar ka ba shi lasisin ya aikata ba daidai ba ne. Ban gamsu da dalilin da suka bayar na cewa gwamnati ba ta da kudi ba ne, in kuwa haka ne a banza ma za a iya kashe makudan kudi a wadansu fannoni da ba su da tasiri a kasa. Ina kira da Sanatoci su gaggauta amincewa da biyan matasa, musamman wadanda ba su da aikin yi alawus din Naira dubu 5 kowane wata don a saukaka musu halin kuncin da suke ciki.”
Ban goyi bayan Sanatoci ba – Malam Usman
Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna
Malam Usman Yusuf: “A ra’ayina game da batun tallafa wa matasa da Naira dubu biyar da Gwamnatin Buhari ta kuduri aniyar yi amma Sanatoci suka ki amincewa. Wannan sam bai dace ba. A gaskiya yunkurin da gwamnati ke yi don tallafa wa matasa da wannan alawus na Naira dubu 5 shi ya fi dacewa don zai taimaka wa matasa wajen rage radadin talauci. Ke nan hana su wannan kudi zai iya jefa su cikin halin kaka-ni-ka-yi da hakan ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba. Mafi yawa daga cikin matasan kasar suna aikata ba daidai ba ne, saboda rashin ayyukan yi da kuma talauci, don haka ni ban goyi bayan abin da Sanatoci suka yi ba.”
Hana tallafin tozarta gwamnati ne – Muhammad Soja
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Muhammad Soja: “A ganina, nuna rashin amincewa da bukatar a rika ba da tallafin kudi, Naira dubu biyar-biyar ga marasa aikin yi a kowane wata a cikin kasar nan da ’yan Majalisar Dattawa suka yi ba komai ba ne illa kokarin kwance wa Gwamnatin Muhammadu Buhari zani ne a kasuwa. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai wannan kudiri, kudiri ne da sabuwar gwamnatin talakawa ta Muhammadu Buhari ta daukar wa kanta, to ai ka ga in an yi hakan tamkar zagon kasa ne ga shi mai girma Shugaban kasa, duk da cewar tattalin arzikin kasar nan na cikin wani hali da gwamnatin baya ta jefa shi. Don haka lallai akwai sake, wato akwai bukatar ’yan majalisun kasa da su sake tunani dangane da wannan lamari; in dai ba so suke yi talakawan kasa su shiga tunanin wani abu daban ba.”
Hana tallafin bai dace ba – Usman Abdullahi
Musa Kutama, a Kalaba
Usman Abdullah dankasuwa: “Gaskiya hakan da suka yi, ni a nawa ra’ayin bai dace ba. Wannan datakatarwar da suka wa shirin ba matasa tallafin Naira 5,000 bai kamata ba. Idan ma da yadda za su yi su amince a rika ba su fiye da haka ma yana da kyau. Don haka ’yan majalisa su sake yin tunani kan haka.”
Hana tallafin ya dace – Abubakar Ali
Musa Kutama, a Kalaba
Abubakar Ali Dawa: “Hanawar da suka yi akwai hikima a ciki saboda halin da kasar nan take ciki na matsalar tattalin arziki. Ina ganin hanawar da suka yi a wannan lokacin ya fi zama daidai. A bari har sai lokacin da kasar nan ta farfado sai a fara bayar da wannan tallafin. Haka ina ganin shi ne daidai.”