✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ko sisi ba a biya ba don sako fasinjojin jirgin kasan Kaduna su 7’

Ya ce in ma iyalansu sun biya kudin, to shi ba shi da masaniya

Tukur Mamu, dan jaridar nan da ya shiga tsakani har aka sako bakawai daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, ya ce ko sisi ba a bayar ba domin sako su.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni suke cewa sai da aka biya Naira miliyan 800 kafin a sami kubutar da mutanen.

A hirar da Aminiya ta yi da dan jaridan, ya ce a iya saninsa, ba a ba wadanda suka yi garkuwa da ‘yan taddan nan ko kwabo don sako mutanen ba daga cikin wadanda su ke garkuwa da su.

Tukur Mamu ya ce, “An dai sako mutanen ne sakamakon rarrashi da ban-baki, da kuma rokonsu na yi ta yi. Domin har kuka na yi musu kan halin da na ga mutanen suna ciki na a sake su.

“Idan watakila iyalan mutanen sun biya wani abu ne ta bayan fage, to ni ban sani ba”.

Da Aminiya ta tambaye shi alakarsu da ‘yan ta’addan da har ta kai ga ya shiga tsakani har aka saki fasinjojin, sai Tukur Mamu ya ce, ba shi da wata alaka da su.

“Sai dai bukatar ta a shiga tsakani ta taso, sai wadanda ake tsare da su din suka bayar da sunana a matsayina na dan jarida,” inji shi.

Domin a cewarsa, jaridarsa Desert Herald ta dade tana kalubalantar gwamnati da kuma fada mata gaskiya komai dacinta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Da ‘yan ta’addan suka ce ba za su tattauna da kowa ba daga gwamnati saboda ba su yarda da su ba.

Wannan, a cewarsa ta sa dole aka shigo da shi, kuma ya yi shahada ya yarda domin ya taimaka a ceci ran wadanda ake rike da su din.

A baya dai Takur Mamu shi da Sheikh Gumi sun yi fice wajen kiraye-kiraye da kuma ganin an bi ta hanyar rarrashi da tattaunawa da ‘yan bindigar don samun masalahar kawo karshen satar mutane da kashe-kashen da ‘yan bindigar ke yi.

Sun kuma rika shiga cikin dazuka suna ganawa da shugabannin ‘yan bindigan suna yi musu wa’azi da nasiha, kan su ajiye makamansu a kuma samu masalaha, a cewarsa.

Daga karshe Mamu ya ce duk wannan abin da ya yi babu sannu ballantana na gode, a maimakon yabo ko makamancin haka sai zargi ne ya biyo baya daga gwamnati duk da cewa duk kai-komon da ya yi har aka sako mutanen, da sojoji aka yi.