✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko sanatocin Kaduna sun so ko sun ki za mu karbo bashi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa duk da kin saka mata hannu da Majalisar Dattawa ta yi, don karbo bashin dala miliyan 350 daga Bankin…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa duk da kin saka mata hannu da Majalisar Dattawa ta yi, don karbo bashin dala miliyan 350 daga Bankin Duniya ba zai hana ta ci gaba da ayyukan raya jihar da ta ke yi ba, sannan za ta yi duk mai yiwuwa wajen cimma burinta.

Kwamishinan Kudi na Jihar, Suleiman Abdu Kwari ne ya furta haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna. Kwamishinan ya ce hujjojin da sanatocin jihar uku suka ba da ba gaskiya ba ne, sannan hakan da suka yi ba zai hana jihar ci gaba da neman wannan bashi ba.

“Mun cika dukkan sharuddan da ake bukata tun daga na Bankin Duniya har zuwa wanda majalisar ke bukata, amma saboda siyasa da son kai na sanatocin jihar uku sun ki mara wa kokarin gwamnatin baya ta samu bashin. Saboda cika sharuddan ne ma ya sa Majalisar Wakilai ta amince da wannan kudiri tun kwanakin baya.

“Wannan bashi za mu yi amfani da shi ne wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar Kaduna, musamman a fannin ilimi da kiwon lafiya da sauransu. Mutanen Jihar Kaduna shaidu ne cewa wannan gwamnati ba gwamnatin kashe-mu-raba ba ce, gwamnatin talakawa ce kuma gwamnatin aiki,” inji shi.