A sha’anin mulkin siyasa a Najeriya, duk wanda Allah Ya bai wa nasarar zama shugaba na kasa ko jiha ko karamar hukuma, yakan zo da irin nasa salon mulki don jagorantar al’ummarsa.
A wasu lokutan musamman kafin a yi zabe, ’yan takarar da suke ganin za su yi nasara sukan kafa kwamitin da zai tsara ya kuma shirya masu daftarin yadda za su tafiyar da mulkinsu tun kafin su samu kujerar ko kuma da zarar sun samu nasara kafin a rantsar da su ko ana rantsar da su.
- Masuntan China na kwace wuraren kamun kifi a Afirka ta Yamma
- Barawon abinci ya kashe manomi a Zariya
Kamar yadda mafi yawan wadanda suka yi nasarar zama Gwamna kan yi a jihohinsu, Jihar Katsina ma ba a bar ta a baya ba, ta fara da batun rufe asusun jiha, tantance ma’aikata, sauke na saukewa ko canjin wajen aiki da sauransu.
Gwamna Dikko Umar Radda bayan ya fara nada wadanda za su yi masa hidima ta fuskar yada labarai a rediyo da talabijin da jaridu da kafar sadarwa ta zamani, abu na gaba da ya yi shi ne rushe duk wani mukamin siyasa da tsohon Gwamna Masari ya nada in ban da na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar da aka canza mata suna zuwa kwamiti.
Wannan mataki bai tsaya a kan nadin mukaman siyasa ba, hatta manyan sakatarorin ma’aikatun jihar abin ya shafe su, domin ya ba su umarnin su mika ragamar mulki ga na kusa da su.
Gwamna Radda ya ce yana yin haka ne don mayar da jihar cikin hayyacinta, har zuwa rubuta wannan rahoton babu wanda zai iya cewa ga wadanda ake zaton za su samu mukamai a gwamnatin.
Babban abin da mutane ke yawan cewa ko nuna fargaba a kai shi ne, yin gwamnatin manyan ’yan boko zalla.
Malam Shu’aibu, wani tsohon ma’aikaci kuma dan siyasa, da wakilinmu ya tuntube shi kan wannan batu da ake yayatawa na yin gwamnatin ’yan boko masu manyan takardu.
Ya ce, “Hakika kowace gwamnati ba laifi ba ne ta tafi da masu ilimi mai zurfi, kuma ba laifi ba ne ta yi tafiya da sauran jama’a.
“ To sai dai mu a nan Jihar Katsina abin kamar shinkafa da wake ake yi. Kowa ya san jiha ce ta ’yan boko da ’yan siyasa wadanda duniya ta san da su.
“Misali, ga irin su marigayi Alhaji Lawal Kaita, ga gidansu marigayi tsohon Shugaban Kasa Malam Umaru Musa ’Yar’aduwa, wanda har gobe gidan siyasa ake kallon su ba na ’yan boko ba.
“Kuma har zuwa yau duk mukaman da suka rike babu wanda zai ce ya ji sun ce ba za su bayar da mukami ba, sai ga masu ilimi mai zurfi ko sai wanda ke da digiri.
“Kamar yadda muka ji an ce shi Gwamnan na yanzu yana son yin salon mulki irin na marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa, to akwai wasu abubuwan da zai yi la’akari da su ko ya yi taka-tsantsan da su.
“Lokacin marigayi Malam Umaru ’Yar’aduwa babu irin mutanen da bai dauko ya sa a cikin gwamnatinsa ba.
“Amma a ce mai son jagorancin jama’a ya ce sai mutane iri kaza ko masu ilimi kaza zai sa a gwamnatinsa?
“In dai har da gaske ne wannan batun ba yarfen siyasa ba ne, to, gaskiya zai fuskanci matsala domin mulki ne na siyasa.
“Ai ko a tsarin mulkin kasa daga bakin mai ilimin sakandare ya ambata wajen shiga zabe ko rike mukamin siyasa.
“Don haka, ina ganin kamar yadda ya sani, mulkin siyasa sai dan siyasa. Kawai abin da ba zan goyi ba shi ne, kada ya yi kuskuren dauko ko da mutun guda daga cikin na baya,” in ji Malam Shu’aibu.
Shi kuwa Alhaji Lawal Kwashi Jibiya matashin dan siyasa daga Jam’iyyar PDP yana ganin yadda Gwamna Dikko Radda yake yi hakan ya fi dacewa da jihar.
“Mu a nan Jibiya babu abin da ya fi addabarmu irin batun tsaro. To tsakani da Allah zan iya cewa, ga alamu zai yi abin da ya dace, musamman game da sha’anin tsaro.
“Yau bai wuce kwana uku ba ’yan sanda da ’yan banga sun shiga dajin nan kuma sun yi aiki. Ka ga a nan sai mu ce mun ga wata alama.
“Sannan batun cewa, za a yi gwamnatin masu digiri da digirgir, ni sai in ce kamar ba haka abin yake ba. An san gwamnati ba za ta tafi ba sai da masu ilimi, to kuwa in haka ne ashe sa masu ilimi shi ya fi dacewa.
“Sai dai kuma a hannu guda yana da kyau a ba ’yan siyasa fiffiko domin mulkin nasu ne, kuma ai a cikin ’yan siyasar akwai masu matakin karatun da ya fi digiri ma.
“Ni har yanzu wannan maganar ta masu digiri ina jin ta ne kawai,” in ji Alhaji Lawal.
Ya ce, babban abin da ya kamata Gwamna Radda ya ba fiffiko a jihar bayan tsaro shi ne batun noma da kiwo.
Ya ce, “Jihar Katsina ta manoman rani da damina ce. Don haka, shigowar gwamnati na da kyau matuka. Sannan batun kiwon lafiya da kasuwanci, muddin aka kula da wadannan abubuwa to an gama yi wa al’umma komai.”
Da ya juya kan batun bayar da mukamai, Alhaji Kwashi ya ce, akwai yiwuwar Gwamnan yana nazarin wadanda zai bai wa mukaman ne.
Sai dai fatarsa, kada a yi zaton wuta a makera ta tashi a masaka.
Ta fuskar yada labarai wanda hakan ne ke sa jama’a sanin halin da gwamnati ke ciki da sanin halin da jama’a suke ciki, a nan wani dan jarida da ya nemi a sakaya sunansa jan hankali ya yi ga Gwamnan, inda ya ce, ‘‘Yana da kyau ya nemi ’yan jaridar da ke jihar don tattaunawa da su ya ji ta bakinsu da kuma sanin abin da ya kamata a yi.
“Amma tsayawa kawai a kan abin da mashawartansa ta wannan kafa suka rubuta gaskiya bai dace ba. Kamata ya yi duk wani aiki da zai fita ko wani muhimmin abu ya taso, ya nemi sauran ’yan jarida.
“Ta haka ne jama’a za su san abin da ake ciki, sannan kamar yadda kowa ya sani ga aikin jarida babu ruwanmu da mara wa wani bangare baya.
“Hakan zai ba shi damar sanin koke ko yabo. Amma yanzu irin labarin da ake turo mana a dandalinmu daga mutanensa suke fitowa.
“Ke nan abin zai zamo kamar amshin Shata. Ba na ce hakan bai yi ba, amma mu rika shiga muna sani, tunda muna nan a kowane bangare.
“Tun lokacin da aka rantsar da shi har zuwa yau, babu inda ya nemi zama da ’yan jarida balle mu san manufofi da kudirorinsa har jama’a su sani.
“Mun sani, sau da yawa mai takara yakan fadi wasu abubuwan da zai yi idan aka zabe shi, amma daga baya ya canza wasu.
“Hakan ke sa wasu su rika korafi, amma ta hanyarmu, jama’a za su san halin da ake ciki,” in ji shi.
A karshe dan jaridar ya shawarci mukarraban Gwamnan ta fuskar yada labarai su shawarci Gwamnan ya rika taro da ’yan jaridar jihar don baje kolin gwamnatinsa ta hanyar amsa wasu tambayoyi ko jin wasu bayanai daga al’umma.