✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ko Kwankwaso da Shekarau sun hade ba za su gagare mu ba —Zaura

Zaura ya ce ba zai yi mamakin hadewar Shekarau da Kwankwaso ba.

Mai neman takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, ya ce jam’iyyar ba za ta yi mamaki ba idan tsoffin gwamnonin jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau sun hada kai domin su yake ta.

Zaura, wanda ya ce Shekarau a matsayin uba yake a wurinsa, ya bayyana zaben shugabannin APC a jihar Kano da bangaren Shekarau ya gudanar da cewa na je-ka-na-yi-ka ne.

A wannan bidiyon, Zaura ya jaddada cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ne jagoran APC a Jihar Kano, kuma ko da Shekarau da Kwankwaso sun hada kai, daidai suke da su.