✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko kana goyon bayan a yanke hukuncin kisa ga barayin gwamnati?

Ban goyin bayan kashe su ba – Alhaji Ibrahim Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja Alhaji Ibrahim Nakumba Lokoja: “Ni dai ba na goyon bayan a…

Ban goyin bayan kashe su ba – Alhaji Ibrahim

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Alhaji Ibrahim Nakumba Lokoja: “Ni dai ba na goyon bayan a yanke wa barayin gwamnati hukuncin kisa ba. Dalilina na fadin haka kuwa shi ne, saboda shari’ar Musulunci ba haka ta tanada a rika yi wa barawo ba. Ni ina ganin abin da ya kamata a rika yi masu shi ne, a yi masu dauri mai tsanani da azabtarwa amma ba kisa ba. Kuma bayan wannan hukunci mai tsanani, sai kuma a kwace kudin da suka sata. Idan an yi haka, kamar ma an taimake su ne ke nan tun daga duniya, domin kuwa koda an yi masu hukunci, idan ba a raba su da dukiyar da suka sata ba, gobe kiyama sai sun biya da ayyukansu masu kyau. Wannan shi ne abin da nake ganin ya dace a yi, amma ba a kashe su ba.”

Ina goyon bayan hukuncin kisa – Malam Yahuza

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Malam Yahuza Lawal Ladan: “Ni dai ina goyon bayan a rika yanke wa manyan barayin gwamnati hukuncin kisa. Domin abin da suka yi ya wuce laifin sata ma kadai, ya hada har da cin amanar dukiyar jama’a da aka hannanta masu su kula da ita. A yayin da suka sace makudan kudi haka, sun haddasa mutuwar wasu da dama, sun hana wasu maganin asibiti, sun hana wasu damar samun ilimi. Don haka, babu abin da ya dace da su sai a yanke musu hukuncin kisa kasai. Hatta shari’ar Musulunci za ta amince a kashe su, domin sun taimaka wajen salwantar rayukan al’umma. Wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari da take kokarin dakile aikin barayin gwamnati, lallai tana bukatar a ba ta goyon baya kuma a taya ta da addu’a. Muna rokon Allah Ya taimaka wa Buhari da mukarrabansa, Ya sanya mu samu kasarmu ta ci gaba da samun yalwar arziki da zaman lafiya.”

Hukuncin kisa ya dace da su – Malam Idris

Abbas Ibrahim dalibi, a Abekuta

Malam Idris Sani Kabo: “Hukuncin kisa abu ne babba amma in aka duba girman laifin barayin gwamnatin da ke yin barazana ga tattalin arzikin kasar nan, yin wannan hukuncin zai zamo tamkar tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro.  Ka ga za a sami karancin masu satar dukiyar jama’a. Duk wanda ya saci miliyan 100 aka yanke mai hukuncin kisa don izna ga na baya tabbas babu laifin yin haka a irin kasa tamu saboda ana yin haka a wasu kasashen.”

Hukuncin kisa bai dace ba – Alhaji Dauda

Abbas Ibrahim dalibi, a Legas

Alhaji Dauda Sulaiman Turaki: “A gaskiya bai dace ba domin a kasar nan ba a hukuncin kisa a dalilin sata, kamata ya yi duk wanda ya yi irin wannan, a yi kokari a tabbatar an kwato duk abin da ya sata sannan a yi masa hukuncin da ya dace da laifinsa; a daure shi na tsawon lokaci koda shekara 20 ne. Rashin daukar wannan mataki a baya shi ke janyo irin wannan,  amma hukuncin kisa sai wanda ya kashe wani, sai dai in kuma sabuwar doka majalisa za ta kawo.”

daurin rai da rai ya kamace su – Malama Nafisa

Halima A. Musa, a Abuja

Malama Nafisa Usman: “Ni a nawa gani, a yi musu daurin raid a rai, domin kuwa Allah dai Ya san iyakar talakawa nawa suka rasa ransu ta dalilin irin satar da suka yi. Wai a ce rai daya ya sace abin da ko jikokinsa ba za su iya cinyewa ba, don rashin imani.”

A hukunta su bisa dokar kasa – Malama Zaliha

Halima A. Musa, a Abuja

Malama Zaliha Musa: “Yau da a ce wadannan kudaden da wadanda suke rike da gwamnati suka yi ta sata, da an yi amfani da su yadda ya dace, da yanzu ba mu samu kanmu a cikin wannan yanayi ba. Haba! ko abubuwan da suka yi ta faruwa na tashin hankali a kasar nan, rashin adalci ne ya haifar da hakan, amma yanzu mun gode Allah da Ya ba mu, shugaba adali. Don haka, nawa ra’ayin shi ne, a hukunta su kamar yadda dokar kasa ta tanadar don na baya su yi hankali, kar a taba barin irin wadannan mutane cikin jama’a don sun riga sun zama gurbatattu, a yi musu daurin da sai rai kan raba.”