Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi.
Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal.
- An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa
- Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai
Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi.
“Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha.
Tun da farko, bayan hukuncin kotun ƙolin, majalisar jihar ta ba gwamnan jihar wa’adin kwana biyu ya sake gabatar da kasafin kuɗi, gayyatar da ya ƙi amsawa.
Daga baya shi kuma gwamnan ya gayyace su gidan gwamnati domin su tattauna, inda su ma suka ce ba za su je ba, domin a kafofin sadarwa suka ga gayyatar.
Ana iya tuna cewa, majalisar ta kuma bai wa Gwamna Fubara wa’adin sallamar da sau naɗe-naɗen da ya yi wanda ba ita ta tantance su ba.
Za a sake zaɓen ƙananan hukumomin Ribas
A makon jiya ne Hukumar zaɓen Rivers ta saka 9 ga watan Agusta a matsayin ranar sake zaɓen ƙananan hukumomi.
Rahotonni sun ambato shugaban hukumar Adolphus Enebeli na sanar da hakan yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a birnin Fatakwal.
Wannan na zuwa ne bayan Kotun Ƙolin Nijeriya ta soke zaɓen da hukumar ta gudanar a ranar 5 ga watan Oktoban 2024.
A gefe guda kuma, majalisar dokokin jihar ta gayyaci shugaban hukumar ya bayyana a gabanta domin yin bayani game da zaɓen.
Wannan dambarwar na zuwa ne a yayin da rikicin siyasa tsakanin gwamnan da tsohon gwamna kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke ƙara ƙamari.
Tun bayan ɗarewar Fubara kan mulki, dangantakar da ke tsakaninsa da magabacinsa ta yi tsami, lamarin da ya haddasa rabuwar kawuna a Majalisar Dokokin jihar.
Wasu ‘yan majalisa sun tsaya tsayin daka domin kare gwamnan, yayin da wasu ke goyon bayan APC da Wike.