✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ko babu Wike PDP za ta ci zabe a Ribas —Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ba shi da tasirin da zai hana Jam’iyyar PDP samun nasara a…

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ba shi da tasirin da zai hana Jam’iyyar PDP samun nasara a zaben 2023.

Sule Lamido ya yi wannan furuci ne a tsokacinsa kan rikicin Wike da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a wani shirin siyasa da wani gidan talabijin mai zaman kansa a Najeriya ya yi da shi.

Lamido ya ce bai ga dalilin tayar da kura da Wiken ke yi a PDP ba, kasancewar halastaccen zabe aka yi a Jam’iyyar kuma Atiku ya yi nasara a kansa.

Ya ce baya ga haka, shi kansa Wiken ya amince cewa zaben babu magudi, don haka bai ga dalilin shure-shuren siyasar da yake yi ba.

“Jam’iyyar PDP kamar kowacce jam’iyya tana da dokokinta da tsare-tsare, kuma a harkar zabe, dole ne wani ya yi nasara wani ya fadi.

“Kuma misali yanzu sai a ce don yana gwanmnan Ribas, shi kadai zai hana PDP nasara?

“Al’uummar Jihar Ribas da dama na cikin jam’iyyar nan tun shekarar 1993, kafin ya san ma zai zama gwamna,” in ji Sule Lamidon.