Wani Dattijo a Jihar Gombe mai suna Injiniya Hadi Usman Jekadafari da ko ajin Firamare bai taba shiga ba a rayuwarsa ya samu nasarar kera jirgin sama da injin Vespa ya kuma kirkiro gidajen rediyo biyu a Jihohin Gombe da Kano. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana yadda ya kirkiri abubuwa 77 cikin shekara 30. Ga yadda hirar ta kasance.
Ko wanene Hadi Usman Jakadafari?
Sunana Injiniya Hadi Usman Jekadafari. An haifeni a unguwar Jekadafari a cikin garin Gombe a shekarar 1953 kuma a nan na girma.
- Mai Martaba: Za a fara daukar sabon fim a kan tarihin Hausawa
- Matasa sun kone ‘matsafa’ a gaban ofishin ’Yan sanda a Ogun
Na shiga sana’ar gyaran rediyo da talabijin, har ta kai na fara kere-kere inda na kera jirgin sama mai injin Vespa, daga baya na bude gidan rediyon Hadi mai zaman kansa da kowa yake iya kamawa a cikin garin Gombe.
Ta yaya ka fara koyon gyaran? Wani ne ya koya maka?
Ko daya, babu wanda ya koya min gyara, kawai tashi na yi na ga ina iya gyaran rediyo da talabijin. Idan wani abu ya daure min kai sai naje wajen masu gyara na zauna idan na gani to har abada wannan abun ya zauna a kwakwalwata ke nan.
An ce ka taba kera jirgin sama. Za mu so jin ta yaya ka kera shi?
Ba shakka na taba kera jirgin Sama da injin Vespa a shekarar 1971 a lokacin ina gyaran Vespa. Jirgin mai farfela a sama da kujerar zama biyu ni da wani muka shiga na tashi da jirgin sama na kewaya garin Gombe, kowa ya gan shi a wajen dawowa ne muka fada kan gidan wani ya murgina damu cikin gidan, daga nan sai na hakura.
Bayan jirgin ya batun gidan rediyon da ka yi?
Bayan jirgin sama na kafa gidan rediyo na kaina wanda har na dauki ma’aikata guda 33 suna aiki a karkashina amma bama yin labarai sai dai karanta katin zabe da wasu shirye-shirye domin a lokacin hukuma ta ce kar muyi labarai domin duk abin da muka karanta aka ji a matsayin labari za a dauka haka ne tunda a gidan rediyo aka ji.
Amma muna yin shirye-shirye masu kayatarwa da sauransu. Rashin tallafi da tsadar kayan aiki suka sa na rufe gidan rediyon, amma kwarin guiwar da na samu a wajen jama’a ne yasa na sake bude wani babba a garin Kano wanda yake cin nisan zango kilomita 44 sannan daga lokacin da na fara kera-kere a 1971 zuwa 2020, na kera abubuwa daban-daban guda 77 da suka shiga kasuwa.
Akwai wani risho mai aiki da ruwan sanyi da na yi, mutane suka gan shi kwanan nan a Talabijin shi ne na 73da na yi, yanzu haka ina kan kirkirar wasu abubuwan daban.
Ko a cikin ’ya’yanka akwai wanda ya gajeka a wannan sana’ar?
Duk ’ya’yana babu wanda bai iya sana’ar da nake yi ba domin yaro tun yana karami idan ya kai minzalin shiga Firamare to wasan kasa ya kare sai koyon sana’a. A lokacin da ya gama sakandare ya gama koyon komai.
Har ’ya’yana mata sun iya sana’ata domin akwai takalma da jakunkuna na mata da suke yi wanda idan aka ce maka daga kasar waje aka yi su za ka yarda saboda amincinsu. Akwai dana Bashir yanzu haka babur din da yake hawa shi ya kera kayansa kuma yana yin ‘power bank’ na kwamfuta wanda yake kai wa sa’a 18 kafin ya mutu, na bature kuma sa’a shida zuwa bakwai yake yi ya mutu.
Ka taba samun tallafin gwamnati a wannan sana’a ta kere-kere da kake yi?
Tallafin shi ne kawai nayi abu suyi mamaki su ce abun ya burge amma ban taba samun komai daga wajensu ba.
Zuwa yanzu akwai wani abu da kasa a gaba da zaka kirkiro?
Ni ban taba zama haka bana tunanin komai ba. A kullum ka gan ni tunani na me zan yi ko me zan kirkiro da zai amfani mutane ko za a kai shi kasuwa a sayar. Bayan risho na ruwan sanyi da na yi shekara biyu da suka gabata na yi wasu abubuwa daban-daban har guda 10.
Ka taba zuwa wata kasa ne dan yin kwas kan kere-kere ko gyaran rediyo?
Eh, na je wasu kasashe nan kurkusa a Afirka, amma ba yin kwas ba, zuwan kashin kaina ne ba kasar ce ta gayyaceni ba. Na je kasashe irin su Nijar da Burkina Faso da Senegal da Jamhuriyar Benin da Mali. Na kan shekara biyu a can, wani wajen shekara daya wata kasar ma watanni amma a Nijar na bude ma’aikata inda har wasu mata biyu suka koyi sana’ar gyaran rediyo da talabijin suka bude wajen sana’ar su kafin na bar kasar.
Duk da cewa baka yi karatun boko ba, an ce har jami’ar ATBU ka taba zuwa don yi musu lakca kan yadda aka yi kaset mai zare da batir, yaya abin yake?
Gaskiya ne ko leka aji ana karatu ban taba yi ba, amma na je Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, na yi lakca a lokacin da na yi bincike na gano cewa Alex Alexandra Volta, ne ya kirkiri batir a shekarar 1777, amma bai damu da ya gano karfinsa ba sai da kasar Scotland ta yi nazari ta gano abubuwa uku da suka yi batir din da yadda ake samar da wutar lantarki da suka hada da Voltage da current da kuma empire.
Ganin ka jima kana gyara kuma kana kere-kere, ko akwai wani akwatin rediyo ko na talabijin da ya kan gagareka gyarawa?
Kwarai kuwa ai ba yadda za ayi a ce mutum ya iya komai, dole akwai abin da zai gagareka, wani lokacin zaka yi ta yi ka gagara, dole ka hakura.
Wane irin kalubale ka taba fuskanta a wannan harkar taka?
Kalubale da yawa domin ita rayuwar kan ta cike take da kalubale
A bangaren nasara fa?
Nasara kam an sameta, domin an kera abubuwa daban-daban har 77, wani guda daya ne kawai yake yi ake ganin ya samu nasara ni kuma har 77 na kera, ai nasara kan an sameta.
Ko injiniya na da iyali?
Kwarai kuwa ina da mata daya da ’ya’ya 11.
Mece ce shawararka ga matasa?
Shawara ta ga matasa ita ce kar mutum ya zauna ba ya sana’ar komai, ya dogara da sai gwamnati ta yi masa. Kuma kar matashi ya raina sana’a komai kankantarta. Duk abin da ka ga wani ya yi kaima ka sa a ranka zaka iya, domin ko ni ma ban yarda da lalaci ko karayar zuciya ba.