✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ko a kujerar guragu yake zai iya mulkin kasar nan – Kyaftin Joseph Din

Wani tsohon soja da ke zaune a Jos a Jihar Filato, Kyaftin Joseph Mangtup Din (mai ritaya) ya ce bai kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya…

Wani tsohon soja da ke zaune a Jos a Jihar Filato, Kyaftin Joseph Mangtup Din (mai ritaya) ya ce bai kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus ba ko da rashin lafiyarsa za ta kai a rika dora shi a kujerar guragu ne, domin matukar yana numfashi hakan za ta hana masu neman yi wa dukiyar kasar nan wa-ka-ci-ka-tashi samun nasara.

Kyaftin Mangtup Din wanda ya ce shi abokin Shugaba Buhari ne tsawon shekara 53, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya lokacin da yake bikin cika shekara 80 a duniya a gidansa da ke Jos.

Ya roki jama’a su yi watsi da kalaman da Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose yake yi a kan Buhari, inda ya ce Gwamnan na yi wadannan miyagun kalamai ne don wata bukata ta siyasa.

Ya ce, “Ban san me yake damun Gwamna Fayose ba da a yanzu ba ya da wata magana face ta batun rashin lafiyar Shugaba Buhari? Me ya sa yake magana a kan rashin lafiyar wani? Shi likita ne? Ina so ya sani ba ya da hurumin da zai rika magana a kan batun lafiya ko rashin lafiyar wani. Ina kira da jama’a su daina saurarensa, domin abin da yake fada ba ya da tushe ballantana makama.”

“Ina so mutane su fahimta ko da Buhari yana kan kujerar guragu ne na tabbata zai iya mulkin kasar nan yadda ya kamata har zuwa lokacin da zai kammala wa’adin mulkinsa. Ta yaya ma zai ce Buhari ya yi murabus? Ina ganin kan Fayose ba kalau ba,” inji Kyaftin Din.

Ya ce maimakon surutan da Fayose ke yi kamata ya yi ya mayar da hankalinsa wajen yin ayyukan da zai ciyar da jiharsa gaba, ba wai ci gaba da surutu ratata babu kan gado ba.

Dangane da batun kiran da wadansu ke yi na a sake fasalin kasar nan kuwa, ya ce ba abin da Najeriya ta fi bukata ba ke nan, domin a yanzu babu abin da kasar nan take bukata face fita daga matsalar tattalin arzikin da ta samu kanta a ciki, idan al’amura suka daidaita sai a tattauna batun sake fasalin kasa.

“A yanzu na fi so a mayar da hankali wajen kwato dukiyar kasar nan da ke hannun mutanen da suka sace ta, sannan a matsa kaimi wajen yaki da matsalar tsaro kama daga Mayakan Boko Haram da masu sacewa da garkuwa da mutane da sauran matsalolin rashin tsaro ke haifarwa,” inji shi.

Game da zargin cewa wadansu tsirari ne suke juya Shugaba Buhari kuwa, sai ya ce idan Buharin da ya sani ne, wanda suka shafe fiye da 53 tare, ba zai taba yarda wadansu tsirari su juya shi ba. “Na shafe shekara 53 tare da Buhari, mun yi aiki tare, mutum ne mai son ganin abubuwa sun tafi bisa tsari da ka’ida. Mutum ko wane ne idan ya nemi ya taka doka, to sai inda karfinsa ya kare. Ba ya da son kai, mutum ne mai tsantseni, ba ya son a tara dukiyar haram, kuma yana da burin kasar nan ta samu ci gaba mai dorewa. Don haka babu wadansu tsirari da za su juya shi, sai dai duk wanda yake tare da shi ya bi dokokinsa masu ma’ana da ya tsara,” inji shi.

Ya roki mutane su ci gaba da yi Shugaba Buhari addu’a samun ingantacciyar lafiya domin ya dawo Najeriya ya ci gaba da aikin da ya sa a gaba na neman ganin al’amura sun daidaita a kasar nan.