✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Klopp zai bar Liverpool a karshen kakar wasanni

Klopp zai bar Liverpool bayan shafe shekara takwas da rabi a kungiyar.

Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp zai bar kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana.

Wannan na zuwa ne bayan kocin ya shafe shekara takwas da rabi a kungiyar, inda ya lashe kofi hudu.

Klopp ya bayyana cewar yana son kowa ya kasance tare a karshen kakar wasanni, inda yake bukatar sauyi a aikinsa.

“Ina son komai. Amma wannan hukunci na yanke shi ne don muradin kaina. Ba ni da matsala da kowa, na zauna a kungiyar nan na tsawon lokaci. Ba zan iya ci gaba da aikin nan ko da yaushe ba.

“Na san idan mutum na son yanke hukunci irin wannan yana bukatar ya yi a kan lokaci,” in ji Klopp.

Liverpool dai na daya a Gasar Firimiyar Ingila, inda kocin mai shekara 56 ke fatan sake lashe gasar kafin karewar wa’adinsa a kungiyar.