✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kishi kumallon mata: Labarin Farida (26)

Bayan an dauke wuta, talabijin ta yi tsita, kawayen biyu, Binta da Saratu sai suka samu kansu cikin wani sabon yanayi. Kasancewar mutumin da suke…

Bayan an dauke wuta, talabijin ta yi tsita, kawayen biyu, Binta da Saratu sai suka samu kansu cikin wani sabon yanayi. Kasancewar mutumin da suke shirin zuwa wurinsa ya mutu, sai suka fara kai-komo da tunanin mataki na gaba da za su dauka.

“Yanzu dandaula ya mutu…ya mutu!” Saratu tana alhini. “Yanzu ina zan sa kaina da wannan cikin da ya kunsa mani? kawata, don Allah ina zan samu rufin asiri?”

A daidai lokacin da take wannan maganar, a tsaye take, hannunta rike da madubi. Kafin kawarta Binta ta maida mata amsar maganganunta, sai kawai ta ga ta fadi kasa rub-da-ciki, bakinta yana ta zubar da wata farar kumfa. Kafin ka ce wani abu, kafafunta suna ta harbawa kamar tunkiyar da aka yanka, ranta na shirin fita daga jikinta.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Mun bani, jama’a a kawo mana dauki!”

Da karfi Binta take furta wadannan kalamai, a yayin da ta dafe kai ta fita waje daga dakin cikin sauri kuma a hargitse. Nan da nan mutanen da ke gidan gaba daya hankalinsu ya juyo zuwa dakin Saratu. Cikin lokaci mahaifiya da baban Saratu, har ma da kanenta suka nufo dakin cikin sauri.

“Me ke faruwa?” Baban Saratu ne ke wannan tambayar, bakinsa wangale cikin mamaki. Ita kuwa Binta ta ci gaba da fadin a kawo dauki, tana yin ishara da dakin kawarta.

“Saratu ce, Saratu ce, tana nan ciki…” Abin da Binta ta fada ke nan, tana kuma nuna dakin da hannu, sai dai ba ta fadi abin da ya faru da ita ba.

Nan da nan mutanen suka durara cikin dakin ba tare da jiran wani abu ba. Suna shiga kuwa sai suka iske Saratu kwance magashiyyan, har yanzu tana ta shure-shure da kafafunta. Nan take suka daga ta zaune suna yi mata fifita. A lokacin da suke kokarin dora ta kan kujerar kushin, sai suka ga jini na zubowa daga kasanta.

“Kai danliti, yi maza ka kira mana Malam Bala, ka ce don Allah ya taimaka da mota, za mu kai yarinya asibiti.” Mahaifin Saratu ne yake umurtar kaninta.

Lokacin da aka isa asibiti, kai tsaye aka ba ta gado, bayan likita ya zo ya shiga aikin duba ta. Ko kafin likitan ya zo, an dauki lokaci mai tsawo ana jiransa, inda wata nas ce ta rika kula da ita. Bayan dan lokaci, sai ya fito da wata doguwar takarda, wacce a cikinta ya rubuta sunayen abubuwan da yake bukatar a sayo masa, wadanda suka hada har da magunguna. Mahaifin Saratu ne ya amshi takardar ya tafi, a yayin da ya bar kawarta Binta tana kula da ita.

 “Ina mijinta yake ne?” Abin da likita ya tambaya ke nan, lokacin da ya kalli Binta, wacce take zaune a kujera a bakin gadon da kawarta ke kwance.

Bai jira ta ba shi amsa ba sai ya ci gaba da magana. “Sai dai a yi hakuri, cikin da take dauke da shi ya zube, a sakamakon kaduwa da firgici da ta samu a lokacin da kuka ce ta fadi kasa.”

“Da gaske, likita?” Da murmushi Binta ta fadi haka, a yayin da likita ya shiga mamaki da ya ga haka.

 “Yaya na ga kina murna da wannan labarin, wanda ya kamata ya a ce na bakin ciki ne.” Inji likita cikin mamaki. “Ba za ka gane ba, amma don Allah ka kasance daya daga cikin wadanda za su rufa wa kawata asiri. Ba ta da miji, saurayinta ne ya yi mata wannan cikin kuma labarin abin da ya faru da shi ne ma ya saka ta cikin wannan larura.” “To fa!” Inji likita, ya yi tsaye sototo kamar wanda aka cire wa lakka.

“Wannan labarin abin farin ciki ne ga kawata da ni kaina. Amma iyayenta ma ba su san tana da cikin nan ba. Babu wanda ya sani, daga ita sai ni, sai kuma saurayin nata, wanda jiya ya rasu. Don haka, don Allah ka bar maganar cikin nan a ranka, kada ma ka bayyana shi ga iyayenta, idan sun zo anjima.

“Shi ke nan, babu komai, Allah Ya kiyaye gaba. Ai duk wanda ya rufa wa dan uwansa asiri, shi ma Allah zai rufa nasa.” Abin da likita ya fada ke nan, a lokacin da ya fita daga dakin jinya, ya nufi ofishinsa.

Za mu ci gaba