✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kishi kumallon mata: Labarin Farida (17)

Ya ku masu bibiyar wannan labari, a makonnin baya muka rika gutsuro maku shi har zuwa lokacin da muka tsaya, musamman saboda hutu da Editan…

Ya ku masu bibiyar wannan labari, a makonnin baya muka rika gutsuro maku shi har zuwa lokacin da muka tsaya, musamman saboda hutu da Editan Shafin ya tafi. Alhamdu lillahi, hutu ya kare don haka za mu ci gaba da zayyano maku shi har zuwa karshe da ikon Allah. Idan mun tuna, mun tsaya ne lokacin da Farida ta yi yaji, ta tafi gidan surukarta, ’yar uwar mijinta, Yaya Asma’u. Mijinta, Alhaji Baba da abokinsa Mamman Tela sun je gidan domin biko. Yanzu ga ci gaba: 

Falon ya yi shiru na takaitaccen lokaci, bayan da tattaunawa ta yi zurfi tsakanin Yaya Asma’u da Baba da kuma abokinsa Mamman Tela. Daga bisani ne ma suka cin ma matsaya cewa a kira Uwargida Farida ta shigo falon domin ci gaba da bitar matsalolinsu gaba daya domin ganin abin da ya kamata a yi domin magance su.

“Yaya, idan muka ce yini za mu yi a nan wurin muna canja miyau kan matsalar nan, ba za mu iya tsinana komai ba.” Mamman ya jawo hankalin mai masaukinsu. “Kamar yadda kika sani, babu zukata biyu da suke tunani iri daya a lokaci daya. Kamar yadda yake tabbas, zo mu zauna, inji masu iya magana, zo mu saba ne. Idan an samu sabani, kamata ya yi a natsu, a yi bincike, a gano inda aka samu sabanin nan, a zauna a samu daidaito da fahimta. Har kullum ta haka ake samun warware al’amari komai tsaurinsa.”

“Yanzu na ji kun fara magana amma da mun tsaya muna ta ketar daji. To yanzu ta ina za mu fara?” Yaya Asma’u ta kalli Mamman, alamar kamar da shi take magana kai tsaye.

“Kamar yadda dukkanmu muka sani, babban makasudin taruwanmu a nan, shi ne dalilin sabani da aka samu tsakanin abokina Baba da mai dakinsa Farida. Abu ya yi tsami har ta gangaro zuwa nan gidanki a matsayinki na yayarmu gaba daya. Yanzu ina ba da shawarar a kirawo ta, ta zo nan mu zauna mu yi tariya da tattauna duk abin da ya je kuma ya dawo har ya haddasa masu sabani. Mu gyara al’amari, a samu sasanci.”

Haka kuwa aka yi, Yaya Asma’u ta mike ta shiga dakinta, bayan wani lokaci suka dawo tare da Uwargida Farida. Bayan ta gaishe da mijinta da abokinsa, ta samu wuri ita ma ta zauna. Falon ya kara samun kansa cikin shiru kuma abin da ya kasance ke nan na tsawon minti daya. Kowa na wurga idanu, yana tsammanin jin magana daga dan uwansa. Har yanzu dai, Mamman ne ya dawo da ruhin zancen.

“Madalla, Yaya ke muke saurare a yanzu, kasancewar ke ce shugabarmu a wannan zama.”

“Haka ne batunka.” Yaya Asma’u ta ambata haka, tare da kallon shiyyar Mamman. “Kamata ya yi mu raba gidan nan zuwa biyu. Kai da abokinka ku kasance a gida daya, ni kuma da kanwata Farida, mu kasance a daya gidan. Ta haka sai mu bincika, mu ga inda muka yi sabani, sannan mu ga inda muke bukatar gyara, mu gyara domin saita tafiyar nan.”

“Madalla, ai kuwa wannan tsari ya yi.” Mamman ya fara magana. “To, da farko sai mu fara tambayar kanmu, shin me ya haddasa sabani da rashin jituwa tsakanin masoya kuma ’yan uwan juna, miji da mata, abokina Baba da kuma uwargidansa Farida? Kamar yadda na sani kuma kamar yadda kafin zuwanmu nan muka tattauna da abokina, abin da ya haddasa matsala tsakanin ma’auratan nan biyu, shi ne batun kara aure da Baba ya bijiro da shi. Idan ba shi ba, ma’auratan suna zaune cikin fahimtar juna.”

“Farida, duk da cewa kin yi mani bayanin komai, amma domin mu samu tabbaci daga gare ki, shin yaya gaskiya ko akasin batun nan? Da gaske maganar karin auren mijinki ne matsala kuma me ya sanya kike ganin cewa wannan matsala ce a gare ki da iyalinki?” Tambayar da Yaya ta yi wa Farida ke nan.

Farida ta dukar da kai, sannan ta fara magana. “Hakika batun auren nan shi ne ya haifar mana da matsala. Ni dai ina da tabbacin muddin ya ce yana kan bakansa game da kara auren nan, to babu wata fahimta da za ta ci gaba da gudana a tsakaninmu.”

“Saboda me kika ce haka?” Mamman ya sake bijirar mata da tambaya.

“Ai an ce Juma’ar da za ta yi kyau, daga Laraba ake gane ta. Tun daga ranar da Daddy ya hadu da yarinyar nan ya fara canza mani fuska, ya canza mani yanayi, ya canza yanayin dawowa gida. Wai yanzu Daddy ne yake zuwa wajen bikin mata, yana kaiwa karfe sha biyun dare a waje. Tun da muka yi aure shekara nawa, muddin dai yana kasar nan ba tafiya ya yi ba, bai taba gota karfe tara a waje ba. Amma yanzu fa?”

Farida na fadin haka sai Baba ya yi zumbur, kamar wanda aka tsira wa allura. Ya cika da mamaki, ya wangale baki kamar wanda yake hamma. Ita kuwa Yaya Asma’u sai ta yi wani murmushi dan kadan. Shi kuwa Mamman sai ya kura wa abokinsa ido. Falon ya sake yin tsit, kamar ta bakin yara, kamar mutuwa ta ratsa!