Yan Najeriya sun shiga cikin rudu da jimami a ranar 15 ga Oktoba bayan bangaren Mamman Nur na kungiyar Boko Haram wanda ake kira da Islamic State West Africa Probince [ISWAP] suka kashe ma’aikaciyar jinkai da take aiki da Kungiyar Bayar da Agaji ta ICRC bayan sun yi garkuwa da ita da sauran ma’aikatan lafiya daga garin Rann na Jihar Borno a watan Maris na bana.
Kisan ya zo ne bayan wa’adin da kungiyar ta bayar na 14 ga watan Oktoba ya kare, kuma ya zo ne kusan wata daya bayan kungiyar ta kashe wata ma’aikaciyar lafiya mai suna Saifura Ahmed bayan gwamnati ta kasa biya musu wasu bukatu kamar yadda suka ce. A wani faifan bidiyo da kungiyar ta wallafa, an nuna yadda suka harbi Hauwa Liman sanye da hijabi da bingida. Shugaban ICRC na yankin, Patricia Danzi ta bayyana kisar gillar da aka yi wa Hauwa a matsayin, “rashin tausayi,” sanan ta ce, “labarin rasuwar Hauwa ya daga mana hankai matuka. Muna kira a kawo karshen wadannan kashe-kashen marasa tushe. Ta yaya za a ce an kashe ma’aikatan lafiya biyu a kusan lokaci daya? Babu dalilin haka.”
“Kashe Hauwa da Saifura ba karamin ta’addanci ba ne ga iyalansu, amma kuma abin zai daga hankalin dubban mutane a Rann da sauran garuruwa da ke fama da rikici da ma yankin Arewa maso Gabas inda kiwon lafiya ke da wahala. Muna kira ga da a saki Alice da Leah da gaggawa kuma cikin koshin lafiya,” inji ta.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lokacin da yake magana da mahaifin Hauwa mai suna Mohammed Liman ta tarho, ya jajanta musu, sannan ya fada masa cewa gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto masa ’yarsa. Ya nuna takaicinsa bisa yadda aka yi ta samun tsaiko wajen ceto ta da ranta. Sannan ya ce bai ji dadin yadda rayuwar ma’aikaciyar lafiyar wadda ta rika taimakon wadanda rikicin Boko Haram ya shafa ta kare a haka ba.
Kashe Saifura da Hauwa ta’addanci ne ba wai ga ’yan uwansu ba, ta’addanci ne ga dubban mutanen Rann da kuma yankin Arewa maso Gabas inda suke aiki ba dare ba rana domin taimakon mutanen da suke bukatar kiwon lafiya matuka. Kungiyar ISWAP ta bayar da dalilinta mara tushe na wannan mummunan aikin da suka yi cewa, “Mun cika alkawarinmu kamar yadda muka dauka ta hanyar kashe wata ma’aikaciyar jinkai, Hauwa Liman,” kamar yadda suka fada a faifan bidiyon. “Mun kashe Saifura da Hauwa ne saboda sun yi ridda sun bar addinin Musulunci. Tun lokacin da suka zabi su yi aiki da Kungiyar Red Cross, babu bambanci tsakanin Red Cross da UNICEF.” Amma abin da ’yan ta’addan suka fada ba gaskiya a ciki domin wani rahoto ya nuna cewa ISWAP din sun bukaci diyya mai yawan gaske ne daga Gwamnatin Tarayya kafin su saki matan da ke hannunsu, wanda kuma ba a cika ba. Wannan ne ya sa suka kashe Musulman da ke hannunsu domin suna tunain cewa yin hakan zai sa a matsa wa Gwamnatin Tarayya ta amince da bukatarsu kafin su saki sauran ’yan matan. ISWAP sun ce za su ci gaba da rike Leah Sharibu, daya daga cikin mata 110 da suka yi garkuwa da su a Dapchi a matsayin baiwa har abada. Ita ma Alice Ngaddah wadda ita ma Kirista ce da ke aiki da UNICEF za ta ci gaba da zama a matsayin baiwa. Mun shiga sawun duniya wajen yin Allah wadai da irin wannan mummunan aiki da aka yi wa wadannan ’yan mata ba gaira ba dalili da sauran daruruwa irinsu wadanda ba a samun labari. Muna kira ga jami’an tsaronmu da su kara dagewa wajen kawo karshen wadannan kashe-kashen a Arewa maso Gabas.
Duk da cewa har yanzu gwamnati ba ta bayyana bukatun da Kungiyar ISWAP ta nema ba, wanda hakan yana da alaka da tsaro, mun yi imanin cewa za ta iya tattaunawa domin ceto sauran wadanda suke wajen Boko Haram din. Amma dai ba mu so gwamnatin ta amince da yarjejeniyar da ka iya kawo koma-baya a yaki da ’yan ta’addan, kamar sakin manyan kwamandojin Boko Haram din da aka kama. Muna jimanin rasuwar wadannan ’yan mata wadanda suka sadaukar da rayuwarsu. Muna da tabbacin cewa mutuwarsu ba zai tafi a banza ba.