Wasu bayanai na ta yawo a kafofin sada zumunta cewa an sauya sunan garin da jirgin sojoji ya kashe ’yan Mauludi daga Tudun Biri an mayar da shi Tudun Mauludi.
A kan hakan ne Aminiya ta nemi karin bayani daga mazauna garin, amma suka shaida mata cewa ba su da labarin canza wa garin nasu sunda ga Tudun Biri suna zuwa Tudun Maulidi.
Wani mabiyin Darikar Tijjaniya a garin Tudun Biri Mai Suna Malam Muhammad Bello Udawa ya bayyana cewa ba su da labarin canza sunan garin da ake cewa an yi bayan harin bom da jirgi ya kai wurin taron Mauludi.
Malam Muhammadu Bello Udawa ya shaida wa Aminiya a ranar Asabar cewa, abin da ya sani shi ne, Shaikh Mansur ne ya taba canza sunan garin zuwa Tudun Faila.
- Hattara: Jabun kudade sun bazu a gari —CBN
- Matatar Man Dangote ta fara tace ganga 1m na danyen mai
- Kasuwar WAPA: Yadda uwar kasuwar canji a Nijeriya ta samo asali
Raha ce
Ya ce, “Shehu Abdul Ahad Nyass, sama da shekaru 20 ya taba kafa makaranta a garin, shi kuma Shehu Mansur ya taba zuwa garin nan Maulidi, yake ce wa mata, ‘ba Tudun Biri ba, saboda Biri saboda Biri ba shi da ma’ana. ‘Mu din nan mun zo ne saboda Annabi, saboda haka za mu mayar da garin Tudun Faila’.
“Matane suka ce da shi yawwa Shehu, dama ka taba zuwa garin nan ka fada mana ba Tudun Biri ba, amma Tudun Faila.
“Matan da bom ya ta da mazajensu ne suka tuna wa Shehu Mansur a lokacin da ya je jaje a garin jiya Juma’a.
“Sai duk muka yi dariya. Wannan abin a gabana aka yi, shi yasa nake maka bayanin abin da ya faru.
“Ga Shehu Mansur, ga Shehu Abdulahad. Saboda haka ni ba labari aka ba ni ba.
“Wannan karamci ne daga wajenmu ’yan darika, amma su a wajen gwamnati ai ba za su canza ba, domin a wurinsu har yanzu Tudun Biri ne sunan.
“Masoya ne suka canza sunan ba gwamnati ba.
Shin Sheikh Dahiru Bauchi ya sauya sunan garin?
Game da ko ana da labarin wai Shaihin Dahiru Bauchi ne ya canza sunan garin sai ya ce “A’a ba ni da wannan labari”
Shima wani mazaunin garin mai suna Bello Tudun Biri, ya ce shi ma ba shi da labari cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya mayar da sunan garinsu Tudun Mauludi.
” Ni ina asibiti tun ranar da abin ya faru saboda haka ba ni da wannan labari.
“Gani na Yi a Facebook wai an ce an canza suna, amma gaskiyar labarin ni ba ni da wannan labari,” in ji shi.