✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban So Ummita Ta Mutu Ba —Dan China

Dan China ya gabatar wa kotu bidiyon kayan bikin aure da ya saya wa Ummita da gidan da take ginawa a Abuja

Dan Chinan nan da ake zargi da yin kisan gilla ga budurwarsa Ummukulsum Sani Buhari da aka fi sani da Ummita, ya shaida wa kotu cewa bai so masoyiyar tasa ta mutu ba.

Mista Frank Geng Quarong shaida wa alkali haka ne a lokacin da aka sake gurfanar da shi a ranar Alhamis a kotun da ke zamanta a Kano.

A zaman kotun na ranar ranar Alhamis, mai gabatar da kara kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Batista M. A. Lawan ya tambaye Mista Quwangrong ko shi ya kashe Ummita?

Shi kuma ya amsa da cewa, “Ni ban so ta mutu ba, kuma ba na so na mutu.”

Idan ba a manta ba, a shari’ar baya, Mista Geng Quangorong da ake zargi da zuwa gidan su Ummita ya yi mata kisan gilla,  yi ikirarin kashe mata kudi sama da Naira miliyan 100 cewa zata ta aure shi, amma daga baya ta juya masa baya, da ta ga ya tsiyace.

Da yake kare kansa a ranar Alhamis, ya gabatar wa kotun wani bidiyon da ya ce Ummita ce ta turo masa na gidan da take ginawa a Abuja.

Kotun ta sanya bidiyon da kuma wani bidiyon kayan bikin da dan Chinan ya yi ikrarin ya saya wa marigayiyar.

Tambayoyin da ka yi wa Dan China

Amma mai gabatar da kara ya tambaye shi dalilin zuwansa gidan su marigayiyar ba tare da an gayyace shi ba, inda ya amsa da cewa dama can ya saba zuwa gidan.

Ya tambaye shi dalilin da bai yi wa mahaifiyar Ummita magana ba a lokacin da ta bude masa gidan, amma ya amsa cewa saboda ba sa fahimtar yaren juna ne.

Game dalilin shigarsa gidan kuwa, amsawa ya yi da cewa ya shiga ne don ya dauki karensa.

Har ila yau an tambayi Mista Geng ko shi ya kashe Ummita? Sai dai amsar wannan tambaya ta gagara, inda ya ce ‘Ni ban so ta mutu ba, kuma ba na so na mutu’.

Daga nan Alkalin Kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage shari’ar zuwa ranar 29 da 30 ga watan Maris, 2023 don ci gaba da sauraren shaidun kariya.

Waiwaye

An gurfanar da Mista Geng Quangrong ne bisa zargin sa da hallaka masoyiyarsa a watan Satumbar 2022, zargin da ya musanta.
A zaman kotun na baya, shaidu da suka hada da mahaifiyar marigayiyar da kanwarta da wasu makwabta sun bayyana wa kotu cewa wanda ake zargin ya je har gidan ne ya yi ajalinta.

A zaman kotun na ranar 12 ga watan Janairu, Mista Frank Geng, ya shaida wa kotu cewa ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ta rasu.

Ya ce tun daga lokacin da ya janye ba ta kudi ta daina kula shi, ta ce dole ya nemi wani aiki da zai rika samun kudi sosai.

Abin da ya hada mu —Dan China

“Sai ta aiko min sako ta Whatsapp cewa ta samu sabon saurayi har ta turo min da hotunan da suka dauka tare, abin da ya bakanta min rai, musamman da na ga sun dauki hoton a cikin motar da na saya mata,” in ji shi.

Mista Geng ya ce a ranar 14 zuwa 15 ga watan Satumba marigayiyar ta ki daukar wayarsa, ko amsa sakonnin tes da ya tura mata, washegari da misalin karfe 8:30 sai ya je gidansu Ummita amma ta ki kula shi.

Rikici a kan kare

“Kafin na je gidan sai da na fara kiran ta a waya inda ta ce na mayar mata dan karenta (Charlie), hakan ya sa na tafi gidansu ana ruwa mai karfi a lokacin, inda na yi ta buga kofar suka ki budewa.

“Sai daga baya kanwarta ta zo ta bude sannan ta dauke karen ta shige da shi cikin gida ta bar ni a tsaye a cikin ruwan sama.

“Hakan ya sa na ci gaba da buga gidan har wani makawabcinsu, Mustapha, ya zo ya yi min magana cewa zai kirawo su su bude min kofa. Amma da ya yi musu waya bai same su ba.

“Na ci gaba da bugawa har mahaifiyarta ta zo ta bude inda na shiga gidan na dauki Charlie a kafadata na juya zan fice daga gidan.

“Sai Ummita ta fito daga falo da sauri ta kulle kofar gidan ta fara zagi na har ta mare ni; mahaifiyarta ta nemi ta daina amma ta ki sauraren ta, ta ci gaba.

‘Ta saba mari na’

“Ba shi ne karon farko da take mari na ba; ta taba mari na a gaban ’yan gidansu da kuma wani lokaci a gaban kanwarta a gidan abinci mai suna Gusto, kasancewarta mai saurin fushi; ko mutanen gidansu sun san halinta na saurin fushi.

“A lokacin ina tsaye a gidan na rasa abin yi saboda ta kulle kofar gidan.

“Daga nan cikin fushi sai ta koma daki ta dauki wuka, hakan ya sa na ji tsoro na ajiye Charlie, na yi kokari na kwace wukar a hannunta.

“Daga nan sai muka fara kokawa inda ta cije ni a hannu da yatsuna, sannan ta rike min gabana sannan ta rika ja na cikin daki, saboda radadin da nake ji sai na bi ta.

“Duk da mahaifiyarta na yi mata tsawa ta bari amma ta ki.

“Sai ta sa kanwarta ta kira ’yan sanda wai zan yi mata fyade kuma za ta kira ’yan immigration su kama ni, daga nan sai ta tura ni kan gado ta ci gaba da zagi na.

“A wannan lokacin ne tabarauna ya bata kuma kasancewar ba na gani sosai idan ba tare da tabarau ba, ga kuma dakin fitilarsa ba ta da haske sosai, ban san yadda aka yi abin da ya faru ya faru ba.”

A cewarsa, “Sai bayan kwana uku wani Aminu ya gaya min labarin rasuwar marigayiyar. Na ji bakin cikin rasuwarta. Abu ne maras dadi.”

Lauyan wanda ake zargi, Barista Danazumi ya shaida wa kotun cewa suna da cikakkun hujjoji da za su gamsar da kotun.

Shi kuma lauyan gwamnati, Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya nemi kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokaci.