Kotu ta ba da umarnin tsare dan kasar Chinan nan da ake zargi da kashe masoyiyarsa, Ummukulthum Buhari a Kano.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta gurfanar da Mista Geng Quanrong a kotu mai lamba 30 da ke Titin Zungeru, kan zargin kisan matashiyar da aka fisani da Ummita, mai shekara 23.
- An Mika ’Yan Matan Chibok 18 Da Aka Sace Ga Iyalansu
- Shugaban ‘yan China ya je ta’aziyyar Ummita Fadar Sarkin Kano
- Buhari zai ciyo bashin N402bn domin biyan bashi
Wanda ake zargin, mai shekara 47 ya bayyana ne a gaban kotun ne a bisa tanadin sashe na 221 na Kundin Pinal Kod.
Sai dai masu gabatar da kara, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano, sun roki kotun ta bayar da umarnin tsare shi kafin lokacin da caji zai fito don gurfanar da shi gaban kotun sama kasancewar ita kotun majistaren ba ta da hurumin gudanar da shari’ar.
Daga nan alkalin kotun, Mai sharia Hanif Khalil Yusuf, ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali tare da dage sauraren shari’ar zuwa 13 ga watan Oktoba, 2022.