Shari’ar zargin Hafsat Suraj (Chuchu) da wasu mutane uku kan zargin kashe wani mutashi mai suna Nafiu Hafiz da ke gaban Babbar Kotun Jihar Kano ta samu tasgaro.
Shari’ar da ke gaban Mai sharia Zuwaira Yusuf na kotun da ke zamanta a titin Miller ya samu tsaiko ne sakamakon rokon da bangaren wadanda ake zargi ga kotun ta sanya musu wata rana da za a karanta wa wadanda ake kara takardar tuhumarsu.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Hafsat Chuchu da mijinta da mai gadinsu da kuma malamin da ake zargi da yi wa gawar Nafiu wanka.
An taba gurfanar da su gaban kotun Majistare da ke zamanta a ’Yankaba karkashin jagorancin Mai Shari’a Hadiza Abdurrahman inda ake tuhumar Hafsat Chuchu da kisan Nafiu Hafiz, sauran mazan kuuma ake tuhumar su da laifin boye gaskiyar dalilin rasuwar Nafiu.
Sai dai lokacin da Gwamnatin Kano ta fara gurfanar da su, dukkansu sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.
Daga bisani aka sanya Talata 6 ga watan Fabrairu, 2024, don sake gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Jihar, amma gurfanarwar ba ta yiwu ba.
Tunda farko bangaren masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Aisha Mahmud sun nemi kotun ta yarje musu musanya takardar karar da wata sabuwa, kasancewar sunan wanda ake zargi na hudu, ba ya cikin tsohuwar takardar rokon da kotun ta amince da shi.
Amma bangaren masu kariya karkashin jagorancin Barista Huwaila Ibrahim Muhammad sun nemi kotun ta sanya wata rana don sake gurfanar da wadanda ake zargin a gabanta domin su da wanda suke karewa na hudu su samu damar yin nazarin takardar karar.
Kotun ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar Alhamis 8 ga watan Fabreru, 2024.